Babu wani shiri da ake na tsige Sarki Sanusi – Gwamnatin Kano

Babu wani shiri da ake na tsige Sarki Sanusi – Gwamnatin Kano

Gwamnatin jihar Kano ta karyata zargin cewa tana shirin tsige Sarkin Kano, Mallam Muhammadu Sanusi II.

Wata kungiyar Kano, ‘The Renaissance Coalition’ tayi zargin cewa gwamnatin jihar na nan tana shirye-shiyen mayar da Sarkin Kano, Mallam Sanusi II zuwa masarautar Bichi.

A wani jawabi dauke da sa hannun kakakin kungiyar, Ibrahim A. Waiya, yayin zargin cewa idan Sarki Sanusi yaki ba da hadin kai, za a tuge shi.

Sai dai kuma, babban sakataren labaran gwamna Abdullahi Umar Ganduje, Alhaji Abba Anwar yayi watsi da ikirarin, cewa babu wani abu makamancin haka ta bangaren gwamnatin jihar.

“Kamar yadda mu muka sani, bamu da masaniya kan wannan lamarin kwata-kwata. A iya sanina babu abu makamancin haka,” inji shi.

KU KARANTA KUMA: PDP ta nemi fadar shugaban kasa ta ba yan Najeriya hakuri kan jawabin Buhari a taron UNGA

A baya mun ji cewa dattawan jahar Kano a karkashin kungiyar sake farfado da martabar jahar Kano sun bankado wata sabuwar kitimurmura da gwamnan jahar Kano, Abdullahi Umar Ganduje yake shiryawa na tsige mai martaba Sarkin Kano, Muhammadu Sunusi II.

Jaridar Daily Nigerian ta ruwaito tun bayan da gwaman jahar Kano ya kirkiri sabbin masarautu guda 4 a jahar Kano, tare da rage ma Sarki Sunusi karfin iko, aka lura Sarkin ya janye daga halartar tarukan gwamnatin jahar.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel