PDP ta nemi fadar shugaban kasa ta ba yan Najeriya hakuri kan jawabin Buhari a taron UNGA

PDP ta nemi fadar shugaban kasa ta ba yan Najeriya hakuri kan jawabin Buhari a taron UNGA

Jam’iyyar Peoples Democratic Party (PDP) ta bukaci fadar shugaban kasa da ta ba yan Najeriya hakuri akan abunda suka kira a matsayin, rashin kokarin Shugaban kasa Muhammadu Buhari a taron majalisar dinkin duniya.

PDP a Wani jawabi daga babban sakataren labaranta na kasa, Kola Ologbondiyan, a ranar Alhamis, 26 ga watan Satumba, tace jawabin Buhari wanda baya bisa kan layi akan sauyin yanayi da kuma sigar da ya amsa tambayar da aka masa kan tanadinsa ga matasa, ya tabbatar da rashin fahimtarsa ga turanci kamar yadda ake bukata a sashi na 318 (iii) na kundin tsarin mulki.

“Maimakon cin mutuncin yan Najeriya, kamata yayi fadar Shugaban kasa ta ba yan kasar mu hakuri akan tozarcin da shugaba Buhari ke janyo na kasar mu," inji jam’iyyar.

Ta kara da cewa “PDP ta lura cewa gazawar shugaba Buhari wajen amsa tambayar da aka masa daidai ya nuna cewa bai halarci makaranta har zuwa matakin sakandare ba, sannan kuma bai mallaki satifiket din WAEC ba, sannan hakan ya kara nuna dalilin da yasa bai sanya kowani satifiket na karatu ba kamar yadda aka bukata a fam CF001 na INEC.”

KU KARANTA KUMA: APC ta musanta cewa ta zabi wanda ta ke son ya yi mata takara a 2023

Amma ofishin labarai na fadar shugaban kasa tace shugaba Buhari ya zabi gabatar da shiryayyen jawabi ne.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel