Kotu ta yankewa tsohon shugaban NBA shekaru 3 a gidan gyaran hali

Kotu ta yankewa tsohon shugaban NBA shekaru 3 a gidan gyaran hali

- Alkalin babbar kotun tarayya da ke Yola jihar Adamawa ta yankewa tsohon shugaban lauyoyin jihar shekaru 3 a gidan maza

- Ta kama lauyan da wanda yake karewa ra'ayi da laifin sata da damfarar ma'aikatan masu murabus na wani kamfani hara N67,000,000

- Hakan kuwa ya saka tsoffin ma'aikatan cikin mummunan halin rashi da matsananciyar rayuwa

Babbar kotun tarayya da ke Yola ta yankewa tsohon shugaban lauyoyin jihar, Binanu Esthon da mai shari'a Shehu Mustapha, shekaru 3 a gidan maza sakamakon kama su da laifin damfara da ta yi.

Hukumar yaki da raashawa ta EFCC ta zargi Esthon da Mustapha da laifuka 7 da suka hada da damfara a 2015.

Mai shari'a Bilkisu Aliyu ta kamasu da laifin sata da damfarar N67,000,000 daga ma'aikata 502 da suka yi murabus na kamfanin Stirling Civil Engineering Nigeria Limited a Adamawa a 2007.

KU KARANTA: Alhakin-kisan-jamal-khashoggi-ya-rataya-a-wuyana-ji-yariman-saudiyya

"Mustapha ya karba kudin ma'aikatan da suka yi murabus tare da kin biyansu hakkokinsu. Shi kuma Esthon a matsayinsa na ma'aikacin shari'a da zai iya tirsasa Mustapha ya biyasu kudinsu ya ki. hakan kuwa ya jefe tsoffin ma'aikatan cikin mummunan hali."

"Mustapha ya aiwatar dda laifin da ya sabawa shari'a gaba daya kuma abin ashsha ne,"

Akan Esthon kuwa, ta ce a matsayinsa na lauyan Mustapha kuma masanin shari'a, ya dace ya tsayawa adalci ne ta hanyar tabbatar da adalcin a matsayinsa na lauya.

Aliyu ta ce, esthon ya taka rawar gani wajen cutar da Mustapha wanda yake jarewa ra'ayi.

Ta ce shekaru uku a gidan maza sune hukuncin da shari'a ta tanadar musu. ta kuma umarci EFCC da ta dau matakan gaggawa na amsowa ma'aikatan mau murabus hakkokinsu.

A maida martanin da hukumar yaki da rashawa ta EFCC ta yi ta bakin lauyanta, Ahmad Muntaka, ta ce adalci ya tabbata a shari'ar.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel