Tirkashi: Jam'iyyar PDP ta bukaci mataimakin shugaban kasa Osinbajo yayi murabus

Tirkashi: Jam'iyyar PDP ta bukaci mataimakin shugaban kasa Osinbajo yayi murabus

- Babbar jam'iyyar adawa ta Peoples Democratic Party (PDP) ta bukaci mataimakin shugaban kasa Yemi Osinbajo da yayi murabus daga kujerar shi

- Jam'iyyar ta bayyana hakan ne a wani martani da ta mayarwa da mataimakin shugaban kasar a wata magana da yayi

- Mataimakin shugaban kasar dai ya bayyana cewa a shirye yake ya jingine kariyar da gwamnati take bashi yaje a bincike shi akan zargin da ake yi masa na cin hanci

Babbar jam'iyyar adawa ta PDP ta mayar da martani akan maganar da mataimakin shugaban Yemi Osinbajo yayi, inda ya ce zai jingine kariyar da gwamnati take bashi yaje a bincike shi akan zargin da ake yi masa.

A sanarwar da babbar jam'iyyar adawar ta fitar wacce Kakakin ta na kasa ya sanyawa hannu, Kola Ologbondiyan, ya roki mataimakin shugaban kasar da idan ya isa yayi abinda ya fada din.

KU KARANTA: Arewa ta na bukatar jagora kamar Kwankwaso - Sheikh Ibrahim Khalil Kano

Jam'iyyar PDP din ta bukaci mataimakin shugaban kasar Yemi Osinbajo da ya jingine kariyar da gwamnati take bashi kamar yadda ya fada, sannan yayi murabus daga kujerar shi yaje a bincike shi akan zargin da ake yi masa na cin hanci.

Jam'iyyar ta ce tunda mataimakin shugaban kasa ya bayyana cewa a shirye yake ya jingine kariyar da gwamnati take bashi to muna so yayi hakan ta hanyar yin murabus daga kujerar shi, saboda babu yadda za ayi a bincike a lokacin da yake da mukamin mataimakin shugaban kasa.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel