Mahaifinta ya sanya ta a mari tare da garkameta na shekaru 2 saboda auren dole

Mahaifinta ya sanya ta a mari tare da garkameta na shekaru 2 saboda auren dole

- Hukumar yaki da safarar mutane ta kasa, reshen jihar Kano ta kama wani mutum mai suna Muhammad Ujudud

- Ujudud ya garkame diyarsa Binta tare da sanyata a mari na shekaru 2 akan kin amincewa da mijin da ya aura mata a dole

- Binta da kaninta sunyi shekaru 2 a garkame inda kanin nata ya rasu kwanan sakamakon matsananciyar yunwa

Hukumar yaki da safarar mutane ta kasa ta kama wani mutum mai shekaru 62 a duniya mai suna Muhammad Ujudud da laifin saka yarinya mai shekrau 16 a mari tare da garkameta na shekaru 2.

Jaridar Daily nigerian ta gano cewa Ujudud, mazaunin kauyen Rinji na karamar hukumar Madobi da ke jihar Kano ya hukunta diyarsa din ne sakamakon kin karbar nijin da ya bata ta dole.

Mahaifin ya garkame Binta har da kaninta a dakuna mabanbanta a cikin gidansa. Majiyarmu ta tabbatar mana da cewa kanin bai dade da rasuwa ba.

KU KARANTA: Adam-zango-ya-rantse-da-al-qurani-don-musanta-zargin-da-wani-malami-ya-yi-masa.

Wani mazauni yankin da ya sanar da labarin a sirrance ga manema labarai, ya bayyana cewa dama can an san mutumin da taurin kan ladaftar da iyalansa ta munanan hanyoyi.

Kamar yadda mazauna yankin suka sanar, Ujudud bai cika ci da yaran da ya garkame ba. A wajen suke fitsari da bahaya.

Binta wacce ta rame ga kuma rashin lafiya, ta samu agajin jami'an NAPTIP ne inda suka garzaya da ita asibiti ta fara samun kulawar likitoci.

A tattaunawar da manema labarai suka yi da daya daga cikin 'ya'yan Ujudud wanda ya tserewa hukuncin mahaifinsa, ya ce "Kanina Shehu ya rasu ne sakamakon azabtarwa da yunwar da mahaifin ya yi masa."

Ya kara da cewa, mahaifiyarsu ta rasu shekaru kadan da suka gabata amma mahaifinsu na zaune yanzu da matar kishiyar mahaifiyarsu.

Shugaban hukumar NAPTIP na jihar, Shehu Umar ya tabbatar da kamawar tare da tsare Ujudud. Ya tabbatar da cewa ana cigaba da bincike.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel