NFF ta fitar da cikakken sunayen 'yan Super Eagles da za su buga wasa da Brazil a watan Oktoba

NFF ta fitar da cikakken sunayen 'yan Super Eagles da za su buga wasa da Brazil a watan Oktoba

Hukumar Kwallon Kafan Najeriya (NFF) a ranar Alhamis 26 ga watan Satumba ta fitar sunayen mutane 23 da ke tawagar Super Eagles da za su kara da tawagar kwallon kafa na kasar Brazil a wani wasan kara dankon zumunci da za su buga a ranar 13 ga watan Oktoban 2019.

Kamar yadda sunayen 'yan wasan da aka fitar ya nuna, an dawo da Ramon Azeez da Abdullahi Shehu yayin da shi kuma Peter Olayinka zai buga wasarsa ta farko a Super Eagles kamar yadda Linda Ikeji ta ruwaito.

Tawagar da Najeriya karkashin kulawar Gernot Rohr sunyi kunnen doki na 2 - 2 a wasar kara dankon zumuncin da suka buga da kasar Ukraine.

DUBA WANNAN: Wani dan kasuwa ya sheka barzahu bayan kammala 'sukuwa' da budurwarsa a otel

Super Eagles za su buga wasan ne da Brazil a ranar 13 ga watan Oktoba a babban filin motsa jiki na Singapore.

Ga dai sunayen tawagar Najeriyan da za su kara da Brazil;

Masu tsaron gida: Ezenwa, Uzoho, Okoye.

Masu tsaron baya: Omeruo, Balogun, Ekong, Aina, Awaziem, Ajayi, Collins.

Masu wasa daga tsakiya: Ndidi, Etebo, Iwobi, Esiti, Aribo, Azeez.

Masu wasa daga gaba: Kalu, Simon, Olayinka, Onuachu, Chukwueze, Osimhen, Emmanuel.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel