'Yan sanda sun dira wata makarantar Islamiyya, sun kama malamai 7, a Kaduna

'Yan sanda sun dira wata makarantar Islamiyya, sun kama malamai 7, a Kaduna

An shiga rudani a unguwar Rigasa da ke yankin karamar hukumar Igabi a jihar Kaduna bayan 'yan sanda sun kai farmaki wata makarantar Islamiyya tare da kama malamai 7 tare da kubutar da yara 300.

'Yan sanda sun ce an ajiye yaran a cikin yanayi mai munin gaske. Zargin da mahukuntar makarantar suka musanta.

Jaridar Daily Trust ta rawaito cewa jami'an rundunar 'yan sanda sun kai samame makarantar Islmaiyyar ne da yammacin ranar Alhamis.

Shehu, wani mazaunin unguwar Rigasa da ke koyar wa a makarantar ya musanta rundunar 'yan sanda a kan halin da daliban ke ciki.

Ya ce babu wani dalibi da ke zaune a makarantar ba tare da amincewar iyayensa ba.

"Abin da suka fada na gaskiya ba ne, babu wani dalibi da ke zaune a makarantar ba tare da amincewar iyayens ba. Sai da iyayen kowanne yaro suka saka hannu a takarda kafin a karbi yaronsu a makarantar, kuma iyayen yara ne ke kawo musu abinci tare da ziyartarsu domin ganin halin da suke ciki," a cewar Shehu.

DUBA WANNAN: An gurfanar da wani mutum mai shekar 35 da ya yi wa diyar yayansa mai shekaru 6 fyade a Kano

Shehu ya kara da cewa jami'an 'yan sanda basu yi musu adalci ba tare da bayyana cewa sun yi matukar mamakin rufe makarantar da rundunar 'yan sanda ta yi.

Kazalika, ya bayyana cewa iyaye da dama sun garzayo zuwa makarantar domin ganin halin da 'ya'yansu ke ciki bayan samun labarin cewa 'yan sanda sun dira a makarantar.

Yakubu Sabo, kakakin rundunar 'yan sanda a jihar Kaduna, ya ce za su mika yaran ga iyayensu bayan sun fara damka su a hannun gwamnatin jiha.

"An ajiye daliban cikin mummunan yanayi da sunan basu ilimin Alqur'ani. Akwai alamun duka a gadon bayan dalibai da yawa, a saboda haka za mu gudanar da bincike domin sanin waye ya mallaki makarantar," a cewarsa.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel