Jam'iyyar PDP tayi tir da zanga-zangar da akayi a kan Ambode a Legas

Jam'iyyar PDP tayi tir da zanga-zangar da akayi a kan Ambode a Legas

- Jam'iyyar PDP reshen jihar Legas tayi tir da zanga-zangar da aka yi a Legas ne neman bincikar tsohon gwamnan jihar, Ambode

- Jam'iyyar ta ce bisa ga dukkan alamu ba don Allah ake son yin bincike ba sai dai kawai domin a ci mutuncin tsohon gwamnan

- Jam'iyyar ta PDP ta bukaci a manta da batun binciken domin hakan ba zai haifa wa siyasar jihar da mai ido ba

Jam'iyyar Peoples Democratic Party (PDP) reshen jihar Legas ta yi Allah wadai da zanga-zangar da aka gudanar a cikin 'yan kwanakin nan a majalisar jihar ne neman bincikar tsohon gwamnan jihar Akinwunmi Ambode.

Sanarwar da mai magana da yawun jam'iyyar, Mista Taofik Gani ya fitar a ranar Alhamis a Legas ta ce zanga-zangar an yi ta ne da mummunan nufi da neman cin mutuncin tsohon gwamnan jihar.

DUBA WANNAN: Wata kungiya ta koka bayan 'yan sanda sun rufe mata masallacin Juma'a a Sokoto

The Punch ta ruwaito cewa wata kungiya mai suna 'Lagos Youth Vanguard' karkashin jagorancin Razak Olokooba da Ibrahim Ekundina sun dira harabar majalisar jihar a ranar Talata inda suke neman a binciki tsohon gwamnan jihar.

Kamfanin dillancin labarai na kasa (NAN) ya ruwaito cewa jam'iyyar ta PDP ta ce irin wannan zanga-zangar ba zai haifar da komi ba illa tayar da hankula al'umma da rashin amincewa da gwamnati.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel