Hameed Ali ya zayyana dalilai biyu da suka sa FG ta rufe iyakokin Najeriya

Hameed Ali ya zayyana dalilai biyu da suka sa FG ta rufe iyakokin Najeriya

Gwamnatin tarayya ta rufe iyakokinta ne domin dalilan tsaro da kuma na tattalin arziki, a cewar shugaban hukumar kwastam na Najeriya, Hameed Ali.

Da yake magana da masu ruwa da tsaki da wakilan hukumomin tsaro a Legas, Ali ya ce gwamnati ba ta rufe iyakokinta domin muzguna kowa ba, tare da bayyana cewa ta yi hakan ne domin kishin kasa.

"Mu burin mu shine ganin cewa kasa ta samu tsaro, rayuwar jama'a ta inganta, sannan tattalin arzikin kasa ya bunkasa.

"An dauki matakin rufe iyakokin ne saboda kishin Najeriya, ba a dauki matakin domin muzguna wa wani ba, sai don kare mutuncin kasar mu," a cewarsa.

DUBA WANNAN: Wata uwa a Najeriya ta fadi dalilin da yasa ta amince dan cikinta ya yi mata ciki

Kamfanin dillancin labarai na kasa (NAN) ya ce daga cikin masu ruwa da tsaki da suka halarci wurin taro da Hameed Ali a Seme da ke jihar Legas akwai jakadan Najeriya a kasar Beni; Kayode Oguntuase, shugaban hukumar kula da shige da fice ta kasa (NIS); Mohammed Babandede, shugaban tawagar jami'an tsaro da ke aiki a kan iyakokin Najeriya; birgediya janar E. A Ndagi da sauransu.

Shugaban hukumar NIS ya ce ana fake wa da damar shigo wa da kaya cikin Najeriya wajen aikata abubuwan da basu dace ba, tare da bayyana cewa an rufe iyakokin domin masu ruwa da tsaki su shiga taitayinsu, su fara biyayya da mutunta dokokin kasa.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel