Karya ne hadimaina basa wasan buya da EFCC - Okorocha

Karya ne hadimaina basa wasan buya da EFCC - Okorocha

Tsohon gwamnan jihar Imo, Rochas Okorocha ya musanta rahotannin dake ikirarin cewa wasu daga cikin hadimansa suna buya don kada hukumar dake yaki da cin hanci da rashawa (EFCC) ta kama su.

Wani rahoton kafofin watsa labarai yayi ikirarin cewa hadiman tsohon gwamnan sun gudu daga jihar don tsere ma kamun hukumar yaki da rashawar.

Amman Okorocha a wani jawabi da hadiminsa, Mista Sam Onwuemeodo ya gabatar ya karyata rahoton.

Yace rahoton dake ikirarin cewa hadimaina sun boye bai ambaci hadiman nawa da suka boye ba.

“Rahoton babu gaskiya a cikinsa saboda ba a ambaci suna ba.

“A cikin labarin ga baki daya, mai rahoton ya gaza ambatan sunan koda daya ne daga cikin hadiman ko jami’in hukumar EFCC wadanda suka zo kama su.

“Haka ma rahoton bai ambaci laifin da hadimaina suka aikata ba wanda yayi sanadiyar shigowar EFCC Imo.”

Ya zargi masu hada rahoton a matsayin masu haddasa munafurci ya kuma siffanta lamarin a matsayin abun bacin rai.

KU KARANTA KUMA: Kafin ku soki Buhari ku tabbata kun yi murabus daga gwamnatina – Umahi ya gargadi hadimansa

A halin da ake ciki, Legit.ng ta rahoto a baya cewa anyi zargin cewa hadiman, tsohon gwamnan jihar Imo, Sanata Rochas Okorocha sun shiga yar buya a Owerri yayin da yawancinsu suka tsere daga garin bayan sake bude shafin bincike da hukumar yaki da cin hanci da rashawa (EFCC) tayi.

Shugaban hukumar yaki da cin hanci da rashawa na reshen kudu maso gabas, Usman Imam a wani jawabi da yayi ga manema labarai a kwanan nan a Enugu, yace hukumar ta sanya alamu akan kaddarori dake da dangantaka da tsohon gwamnan, iyalensa da wasu hadimansa, wadanda ake tunanin sun mallaka ne daga kudaden al’umma da suka sace.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel