Kafin ku soki Buhari ku tabbata kun yi murabus daga gwamnatina – Umahi ya gargadi hadimansa

Kafin ku soki Buhari ku tabbata kun yi murabus daga gwamnatina – Umahi ya gargadi hadimansa

Gwamna David Umahi na jihar Ebonyi a ranar Alhamis, 26 ga watan Satumba, ya bayyana cewa zai tsige duk hadiminsa da ya ci ma Shugaban kasa Muhammadu Buhari mutunci.

An zabi Umahi ne bayan yayi takara a karkashin inuwar jam’iyyar Peoples Democratic Party (PDP) mai adawa.

Har ila yau Umahi ya sha alwashin cewa zai sallami duk hadiminsa da ya kuskura ya ci mutuncin wani gwamna ko kuma ya raina nasarorin da suka samu.

Gwamna Umahi ya fadi haka ne a wani jawabi wanda mataimakinsa na musamman kan kafofin watsa labarai na zamani, Mista Francis Nwaze ya sanya hannu ya kuma gabatar ga manema labarai a Abakaliki.

Jawabin ya dauko daga Umahi yayin da yake cewa hakan shine gargadi na karshe da zai yi ga hadimansa da duk wadanda suka kasance a gwamnatinsa.

KU KARANTA KUMA: Yan fashi sun kai hari wani banki a Ekiti, sun kashe jami’in dan sanda sannan suka tsere da kudade

A wani labari na daban, Legit.ng ta rahoto cewa gwamnonin jam'iyyar APC sun ce karya ne babu wata rashin jituwa da ke tsakanin shugaban kasa Muhammadu Buhari da kuma mataimakinsa, Farfesa Yemi Osinbajo.

Sabanin yadda ake ikirari a wasu lunguna da kafofin sadarwa na kasar nan, gwamnonin APC sun ce maganar rashin 'yar ga maciji tsakanin Buhari da mataimakin sa ba gaskiya bace, lamarin da ya ce in hakan ta kasance babu fadar shugaban kasa kenan a kasar.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel