Yan fashi sun kai hari wani banki a Ekiti, sun kashe jami’in dan sanda sannan suka tsere da kudade

Yan fashi sun kai hari wani banki a Ekiti, sun kashe jami’in dan sanda sannan suka tsere da kudade

Yan fashi da makami sun kai mamaya wani banki a Ise Ekiti, a ranar Alhamis 26 ga watan Satumba, inda suka kashe wani jami’in dan sanda sannan suka tsere da wasu kudade da ba a bayyana ba.

An tattaro cewa fashin ya afku ne da misalin karfe 2:30 na rana inda suke ta harbi yayinda tawagarsu na mutum 10 suka shiga cikin bankin na zamani.

Jaridar premium Times ta ruwaito inda idanun shaida kecewa yan fashin sun kwashe akalla mintuna 25 suna fashi bayan sun shigo garin cikin motoci biyu ta hanyar Ikere.

Kakakin yan sandan jihar Ekiti, Mista Caleb Ikechukwu wanda ya tabbatar da faruwar lamarin yace yan ta’addan sun fasa kofar tsaro na bankin da nakiya sannan suka samu damar shiga ciki.

Yace jami’an rundunar na kan bin sahun yan ta’addan sannan yayi kira ga mazauna jihar da kada su sanya tsoro a zukatansu.

KU KARANTA KUMA: Yan sanda za su fara kama yan siyasan da ke tuki da rufaffen lambar mota

A wani lamarin kuma, mun ji cewa rundunar 'yan sanda reshen jihar Taraba ta ce ta kashe wani gawurtaccen dan fashi da makami da ta dade tana nema ruwa a jallo.

A sanarwar da mai magana da yawun rundunar na jihar Taraba, David Misal ya fitar, ya ce an yi nasarar kashe dan fashin ne bayan an sanar da 'yan sanda cewa wasu 'yan bindiga sun tare hanyar Jatau/Borno kuru-Ku a karamar hukumar Bali na jihar Taraba suna yi wa mutane fashi.

A cewar sanarwar, 'yan sandan tare da hadin gwiwa 'yan kungiyar sa kai sun garzaya inda lamarin ke faruwa kamar yadda Channels TV ta ruwaito.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel