Buhari vs Atiku: APC ta bukaci kotun koli tayi fatali da shaidun da Atiku ya gabatar a kotun karar zabe

Buhari vs Atiku: APC ta bukaci kotun koli tayi fatali da shaidun da Atiku ya gabatar a kotun karar zabe

Jam'iyyar All Progressives Congress (APC) ta bukaci kotun koli tayi watsi da hujjojin da lauyoyin Atiku suka gabatar a kotun sauraron karrakin zaben shugaban kasa na zaben 2019.

Channels TV ta ruwaito cewa jam'iyyar ta APC tayi hakan ne domin takawa jam'iyyar PDP da dan takararta Atiku Abubakar birki a karar da suka shigar a kotun kolin.

APC ta shigar da karar neman kotun tayi watsi da rahoto da hujojji da kwararrun shaidun uku suka bayar da shaida a madadin jam'iyyar PDP a kotun sauraron karar zaben shugaban kasa.

Lauyan jam'iyyar APC, Prince Lateef Olasunkanmi Fagbemi (SAN) ne ya shigar da karar na neman watsi da shaidan da Segun Sowunmi da David Njoga da Joseph Gbenga da Atiku ya dauka a matsayin kwararru masu binciken kwakwaf.

DUBA WANNAN: 'Yan sanda sun kashe wani gawurtaccen dan fashi da ake nema ruwa a jallo

A shaidan da suka bayar, sunyi ikirarin cewa anyi wasu 'yan dabarbaru an rage wa Atiku kuri'unsa yayin da shi kuma Buhari aka kara masa kuri'un.

Daya daga cikin shaidun dan asalin kasar Kenya ya yi ikirarin cewa INEC tana da wani rumbun ajiyar sakamakon zabe na intanet da ya yi kutse ciki kuma ya gano ainihin sakamakon zaben da ke nuna cewa Atiku ne ya lashe zaben na ranar 23 ga watan Fabrairu.

Amma Mister Fagbemi ya roki kotun kolin tayi watsi da wannan hujjojin da shaidan da shaidun uku suna bayar ciki har da faifan bidiyo da aka gabatarwa kotu.

Mister Fagbemi kuma ya son kotun ta yanke hukuncin cewa ba za a taba saka amfani da wannan hujjojin da shaidun a kotu ba.

Jam'iyyar ta APC ta ce kotun zaben tayi kuskure lokacin da ta ce za a saurari shaidun da hujjojin domin yi wa dukkan bangarorin adalci.

Babban lauyan ya kuma nemi kotun kolin tayi watsi da zargin da Atiku ya yi na cewa an tafka magudin zabe a wasu jihohi 10 domin masu shigar da karar ba su fadi takamamen rumfar zaben da akayi magudin ba saboda haka shaci fadi ne kawai.

A ranar 23 watan Satumba, Atiku ya daukaka kara a kotun koli inda ya gabattar da hujojji 66 da ya ke rokon kotun tayi amfani da su domin soke zaben shugaba Muhammadu Buhari.

Jam'iyyar na PDP ta nuna kin amincewar ta da hukuncin da alkalan kotun zabe karkashin Mohammed Garba suka yanke na cewa babu bukatar Buhari ya sanya kofin takardun karatunsa cikin fom CF 001 na INEC kafin tsayawa takarar shugaban kasa.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel