Daga karshe El-Rufai ya fara biyan karancin albashi a jahar Kaduna

Daga karshe El-Rufai ya fara biyan karancin albashi a jahar Kaduna

Daga karshe gwamnanatin jahar Kaduna ta fara biyan karancin albashin N30,000 kamar yadda gwamnan jahar, Nasir Ahmad El-Rufai ya yi alkawari tun a farkon watan Satumba.

Legit.ng ta ruwaito gwamnan jahar Kaduna ne ya bayyana haka a shafinsa na kafar sadarwar zamani ta Facebook, inda yace: Mun yi alkawari za mu fara biyan mafi karancin albashi a wannan wata na Satumba, kuma cikin ikon Allah mun cika wannan alkawarin.”

KU KARANTA: El-Rufai zai samar da jiragen sama guda 2 domin jigilar fasinja zuwa Abuja

Daga karshe gwamnan ya bayyana godiyarsa ga al’ummar jahar Kaduna bisa irin goyon bayan da suka baiwa gwamnatin nasa, sa’annan ya yi fatan Allah Yasa a cigaba da musu addu’a.

“Muna godiya ga al’ummar Jihar Kaduna na irin goyon bayan da ake ba mu. Muna fatan za a a ci gaba da yi mana addu’a domin mu sauke duk nauyin da Allah ya daura mana.” Inji shi.

A wani labarin kuma, Gwamnan jahar Kaduna, Malam Nasiru Ahmad El-Rufai ya rattafa hannu kan wata yarjejeniya tsakanin gwamnatin jahar da kamfanin jirgin sama ta Quorum Aviation Ltd, QAL, domin samar da jiragen sama guda 2 da zasu yi safarar Kaduna zuwa Abuja, Kaduna zuwa Legas.

A cikin yarjejeniyar da aka shiga, kamfanin za ta yi safarar jirage sau biyu a rana, kuma sunan da za’a kira jiragen shi ne ‘Boku Air’.

Gwamna El-Rufai ya bayyana cewa yana da tabbacin wadannan jirage zasu rage rububin da jama’a ke yi na bin jirgin kasan Kaduna zuwa Abuja. “Ina da tabbacin kamfanin jirgin zaizo da amfani sosai.

“Don haka nake kira ga yan kasuwa maza da mata dasu ci gajiyar wannan tsarin tafiya a jirgin sama, mun kuma gode ma kamfanin QAL bisa gamsuwa mu kulla wannan yarjejeniya dasu, don haka zamu mika musu titin jirgin da muka gina, muka kuma sanya kayan aiki da kudinmu.” Inji shi.

Ku biyo mu a https://facebook.com/legitnghausa

ko a http://twitter.com/legitnghausa

KU LATSA: Hanyar sauko da sabuwar manhajar jaridar Legit.com Hausa cikin sauki

Ga masu shawara ko korafi, a same mu a labaranhausa@corp.legit.com

Sanarwa na musamman: Shafin NAIJ Hausa ya koma Legit Hausa

Asali: Legit.ng

Online view pixel