Yan sanda za su fara kama yan siyasan da ke tuki da rufaffen lambar mota

Yan sanda za su fara kama yan siyasan da ke tuki da rufaffen lambar mota

Rundunar yan sanda a ranar Alhamis, 26 ga watan Satumba, ta gargadi yan siyasa da masu motoci da su daina rufe lambar mota ko kuma su fuskanci hukuncin doka.

Gargadin ya zo ne a wani jawabi da kakakin yan sanda reshen Jos, Mista Mathias Tyopev yayi a ranar Alhamis.

Kakakin rundunar yace gargadin ya zama dole saboda barazanar da lamarin tsaro ke fuskanta, wanda ya kasance barazana ga mutanen jihar musamman ga taimaka ma harkar garkuwa da mutane da kuma masu fashi da makami a jihar.

Mathias yace “Rundunar yan sandan jihar Plateau tana bayyana bakin cikinta akan al’amuran dake wakana kwanan nan inda wasu mutane, yan siyasa, jami’an gwamnati da sauran su suke rufe lambobinn motocinsu yayin da suke tuki a manyan tituna da kuma cikin gari.

"Wannan ya sa yan sanda cikin wahala musamman wajen yaki da masu garkuwa a mutane da kuma yan fashi da makami."

KU KARANTA KUMA: Kotu ta yanke wa uba da dansa hukuncin kisa a jihar Zamfara

Jawabin ya kara da shawartan al’umma da su kasance masu biyayya ga doka, inda ya kara da cewa ana sa ran masu amfani da hanyoyi za su bi dokar titi yayin da nan da sati biyu yan sandan zasu soma aiwatar da doka a fadin kasar.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel