Kotu ta yanke wa uba da dansa hukuncin kisa a jihar Zamfara

Kotu ta yanke wa uba da dansa hukuncin kisa a jihar Zamfara

Wata babbar kotu na 3 a Gusau, jihar Zamfara a ranar Alhamis, 26 ga watan Satumba, ta yanke wa wani Ibrahim Hamda na kauyen Gobirawa da ke karamar hukumar Tsafe na jihar da dansa, Ashiru Ibrahim, hukunci kisa kan aikata kisan kai.

Masu laifin biyu a cewar alkalin kotun, Justs Muktari Yusha an fara gurfanar da su a gaban kotun a 2018 akan tuhume-tuhume biyu na hada kai wajen ta’addanci da kuma kisan kai a karkashin sashi na 221 na doka.

Alkalin ya zartar da cewa an samu uba da dan nasa da laifin tuhume-tuhumen da ake masu sannan an yanke masu hukuncin kisa.

Yusha yace: “An yanke masu hukuncin kisan kai ta hanyar rataya har sai an tabbatar da sun mutu.”

Masu laifin biyu sun soki wani Rabi’u Tudu na wannan kauyen da wuka wanda yayi sanadyar mutuwarsa.

KU KARANTA KUMA: Miji, mata da jaririnsu sun mutu a cikin gidansu da wasu saka wa wuta a Kano

A wani labarin kuma mun ji cewa Ofishin ‘yan sandan Kuje dake Abuja a ranar Alhamis 26 ga watan Satumba, 2019 sun tura Mubarak Sani dan shekara 27 kotun Majistare a dalilin satar wayar hannu da na’urar chajin waya wato power bank wanda aka kiyasta kudinsu kimanin N250,000.

Sani wanda ke zaune a Anguwan Gade dake Abuja yana fuskantar laifuka guda biyu na sata da kuma ha’inci.

A cewar wadda ta kai karar gaban kotu, Doris Okoroba, wani Sule Bala ne wanda ke zaune a anguwa daya da Mubarka ya kai karar ofishin ‘yan sandan Kuje ranar 19 ga watan Satumba.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel