Wani matashi ya gurfana gaban kotu a dalilin satar wayar hannu

Wani matashi ya gurfana gaban kotu a dalilin satar wayar hannu

Ofishin ‘yan sandan Kuje dake Abuja a ranar Alhamis 26 ga watan Satumba, 2019 sun tura Mubarak Sani dan shekara 27 kotun Majistare a dalilin satar wayar hannu da na’urar chajin waya wato power bank wanda aka kiyasta kudinsu kimanin N250,000.

Sani wanda ke zaune a Anguwan Gade dake Abuja yana fuskantar laifuka guda biyu na sata da kuma ha’inci.

A cewar wadda ta kai karar gaban kotu, Doris Okoroba, wani Sule Bala ne wanda ke zaune a anguwa daya da Mubarka ya kai karar ofishin ‘yan sandan Kuje ranar 19 ga watan Satumba.

KU KARANTA:Sarkin Dutse ya yabawa gwamnatin Najeriya bisa rufe kan iyaka da ta yi

“Bala ne ya kawo karar Sani da wasu mutum biyu wadanda suka shiga shagon sayar da wayoyi suka dauke wayar salula da abin chanjin waya da kudinsu ya kai N250,000.

“Wannan laifin ya ci karo da sashe na 96 da 287 na kundin Penal Code,” inji matar. A bangaren wanda ake tuhumar kuwa ya ki amsa laifin nasa.

Alkalin kotun, bayan sauraron bayani daga bangarorin biyu ya dage sauraron karar zuwa ranar 29 ga watan gobe.

Kamfanin dillancin labaran Najeriya NAN ne ya fitar da wannan labarin.

A wani labarin kuwa zaku ji cewa, Sarkin Dutse ta jihar Jigawa ya yabawa gwamnatin Najeriya game da rufe kan iyakar kasar da tayi, inda ya ce hakan abu ne mai kyau ga tattalin arzikin Najeriya.

Alhaji Muhammdu Nuhu Sanusi ya furta wadannan kalaman ne a lokacin da yake karbar bakuncin kungiyar makiyaya ta Miyetti Allah a fadarsa ranar Alhamis 26 ga watan Satumba, 2019.

Ku biyo mu a https://facebook.com/legitnghausa

ko a http://twitter.com/legitcomhausa

KU LATSA: Hanyar sauko da sabuwar manhajar jaridar Legit.com Hausa cikin sauki

Ga masu shawara ko korafi, a same mu a labaranhausa@corp.legit.com

Sanarwa na musamman: Shafin NAIJ Hausa ya koma Legit Hausa

Asali: Legit.ng

Online view pixel