Babu wata baraka a fadar shugaban kasa – Gwamnonin APC

Babu wata baraka a fadar shugaban kasa – Gwamnonin APC

Gwamnonin jam’iyyar All Progressives Congress (APC) mai mulki, sun yi watsi da rahotannin baraka tsakanin Shugaban Kasa Muhammadu Buhari da mataimakinsa, Farfesa Yemi Osinbajo.

gwamnoniin jam'iyyar mai mulki sun bayyana dukkanin hasashen a matsayin “gulma” da gutsiri-tsoma.

Yayin da suke magana a taron rantsar da kwamitin Gwamnonin APC kan kafofin watsa labarai da sadarwa, Gwamnan jihar Legas, Babajide Sanwo-Olu ya kara da cewa a jiya Laraba, 25 ga watan Satumba, ne mataimakin shugaban kasa ya jagoranci zaman majalisar zartarwa.

Yace a matsayinsu na gwamnoni, suna amfani ne da shaidu ba cece-kuce ba, yayinda ya bukacin yan Najeriya da su cigaba da mara ma gwamnatin Buhari baya.

KU KARANTA KUMA: Buhari ya jinjinawa Bill Gates da Dangote akan aikin alkhairin da suke yiwa yan Najeriya

A baya mun ji cewa daya daga cikin manyan jaridu a Najeriya, Vanguard, ta nemi gafarar mataimakin shugaban kasa Farfesa Osinbajo biyo bayan kuskuren da ta tafka na wallafa wani rahoto marar tabbas da ke yin kazafi a gare shi gami da bata masa suna.

Jaridar Vanguard ta nemi gafarar Osinbajo bayan da ta wallafa wani rahoto da ya ke nuni da cewa, mataimakin shugaban kasar ya karbi kimanin naira biliyan 90 a hannun hukumar tattara haraji ta kasa wato FIRS domin yin kamfe a zaben 2023.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel