Wata sabuwa: Tsoffin hadiman Okorocha sun shiga yar buya yayinda ake cigaba da bincike - EFCC

Wata sabuwa: Tsoffin hadiman Okorocha sun shiga yar buya yayinda ake cigaba da bincike - EFCC

Rahotanni sun kawo cewa hadiman, tsohon gwamnan jihar Imo, Sanata Rochas Okorocha sun shiga yar buya a Owerri yayin da yawancinsu suka tsere daga garin bayan sake bude shafin bincike da hukumar yaki da cin hanci da rashawa (EFCC) tayi.

Shugaban hukumar yaki da cin hanci da rashawa na reshen kudu maso gabas, Usman Imam a wani jawabi da yayi ga manema labarai a kwanan nan a Enugu, yace hukumar ta sanya alamu akan kaddarori dake da dangantaka da tsohon gwamnan, iyalensa da wasu hadimansa, wadanda ake tunanin sun mallaka ne daga kudaden al’umma da suka sace.

Ya bayyana cewa za a gudanar da cikakken bincike kan shekaru takwas da Okorocha yayi yana mulki, yayin da ya bayyana cewa yawancin jami’ai da yan kwangila wadanda suka yi aiki a gwamnatin zasu samu gayyata don amsa tambayoyi.

EFCC ta fara farautarsa da ahlinsa ne a lokacin da ya sauka daga mulki.

Banda rufe wassu daga cikin kasuwancinsa, hukumar ta tura tsare-tsaren kotu don tabbatar da kwace kadarorinsa, wadanda suka hada da makarantu, asibitoci da gidaje, har da asibitin zamanin da tsohon hadiminsa ya mallaka.

KU KARANTA KUMA: Buhari ya jinjinawa Bill Gates da Dangote akan aikin alkhairin da suke yiwa yan Najeriya

Jaridar Daily Sun ta ruwaito cewa an ga jami’an hukumar suna zirga zirga a Owerri, inda hakan ya tilasta wasu sanannun tsoffin hadiman tsohon gwamnan kaura daga wuraren da ake iya ganinsu.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel