Za mu saki Sowore saboda yin biyayya ga umarnin kotu – Minista Malami

Za mu saki Sowore saboda yin biyayya ga umarnin kotu – Minista Malami

Gwamnatin Najeriya a karkashin jagorancin shugaban kasa Muhammadu Buhari ta yi alkawarin sakin matashin dan siyasar nan kuma dan gwagwarmaya, Omoyele Sowore, kamar yadda wata babbar kotun tarayya ta bukata.

Rahoton gidan rediyon BBC ta ruwaito ministan Shari’a kuma babban lauyan Najeriya, Abubakar Malami ne ya bayyana haka cikin wata hira da ya yi da gidan rediyon, inda yace gwamnati za ta yi biyayya ga umarnin kotu wajen sakin Sowore wanda ya kwashe kwanaki fiye da 50 a hannu.

KU KARANTA: Barin zance: Yadda hadimin Ganduje ya ‘kaskantar’ da mataimakin shugaban kasa Osinbajo

Majiyar Legit.ng ta ruwaito a farkon makon nan ne wata babbar kotun tarayya dake zamanta a babban birnin tarayya Abuja ce ta umarci hukumar tsaro ta farin kaya, DSS, da ta saki Sowore, wanda shi ne mawallafin kamfanin jaridar Sahara Reporters.

Wannan hukunci ya biyo bayan janye bukatar cigaba da rike Sowore da hukumar DSS ta yi ne a gaban kotun, amma dai kotun ta sanya sharadin samun beli daga DSS ga Sowore, inda ta umarceshi ya ajiye fasfonsa na tafiye tafiye.

A wani labari kuma, guda daga cikin hadiman gwamnan jahar Kano, Abdullahi Umar Ganduje, ta bangaren watsa labaru, Salihu Tanko Yakasai ya kira ruwa da wata kasassaba daya tafka a shafin kafar sadarwar zamani ta Twitter, inda ya yi ma mataimakin shugaban kasa Osinbajo shagube.

Yakasai ya bayyana mataimakin shugaban kasa Farfesa Yemi Osinbajo ne a matsayin ‘Mataimakin shugaban kasa mai kula da al’amarin karatu’ ta shafinsa mai adireshi @dawisu.

Yakasai ya fadi haka ne yayin da yake mayar da martani ga batun da wani ma’abocin Twitter mai suna Ismail Kabir ya yi, inda yake cewa “Da alama duk wani mai fada a ji a Najeriya ya tafi New York domin halartar taron majalisar dinkin duniya.”

Ku biyo mu a https://facebook.com/legitnghausa

ko a http://twitter.com/legitnghausa

Ga masu shawara ko korafi, a same mu a labaranhausa@corp.legit.com

Sanarwa na musamman: Shafin NAIJ Hausa ya koma Legit Hausa

Asali: Legit.ng

Online view pixel