Ina sha’awar rabar da rabin arzikin da Allah Ya ba ni don taimakon jama’a – Dangote

Ina sha’awar rabar da rabin arzikin da Allah Ya ba ni don taimakon jama’a – Dangote

Attajirin nahiyar Afirka, Aliko Dangote ya bayyana cewa yana sha’awar rabar da rabin dukiyar da Allah Ya yi masa don taimaka ma al’umma musamman a bangaren kiwon lafiya, kuma yana fata Allah Ya cika masa burinsa.

Jaridar Premium Times ta ruwaito Dangote ya bayyana haka ne a ranar Laraba, 25 ga watan Satumba yayin da yake tattauna da kwararru a yayin wani taron kara ma juna sani na Goalkeepers a birnin New York inda yace:

KU KARANTA: Barin zance: Yadda hadimin Ganduje ya ‘kaskantar’ da mataimakin shugaban kasa Osinbajo

“Ina fatan lokaci zai zo da zan rabar da rabin dukiyana ga ayyukan taimako kamar yadda Bill Gates da matarsa Melinda suka yi.”

Dangote ya tabbatar ma mahalarta taron cewa bai san mawuyacin halin da fannin kiwon lafiya yake ciki a Najeriya ba har sai da ya hadu da mai kudin duniya, Billa Gates, duk kuwa da cewa tun a shekarar 1994 yake tallafa ma jama’a da gidauniyarsa ta Dangote Foundation.

Majiyar Legit.ng ta ruwaito Dangoet ya yi magana a kan matsalar rashin samun ingantaccen abinci ga kananan yara a nahiyar Afirka, musamman ma a Najeriya, wanda yace hakan ya samo asali ne daga karancin abinci mai gina jiki, da rashin sinadaran masu bada lafiya a jiki a cikin abincin da yara ke ci.

Don haka yace akwai bukatar a yi gaggawar magance matsalar rashin ingantaccen abinci tun kafin matsalar ta gagari kundila, daga cikin hanyoyin magance matsalar da Dangote ya fada akwai yin dokoki da daga bangaren gwamnati da za su tilasta ma kamfanonin sarrafa abinci inganta abincin da suke yi.

Daga karshe yace sun fara magana da gwamnatin Najeriya don inganta shinkafar da ake sarrafawa a gida da wadatattun sinadaran abinci masu gina jiki, duba da cewa shinkafa ce abincin a aka fi ci a Najeriya.

Ku biyo mu a https://facebook.com/legitnghausa

ko a http://twitter.com/legitnghausa

KU LATSA: Hanyar sauko da sabuwar manhajar jaridar Legit.com Hausa cikin sauki

Ga masu shawara ko korafi, a same mu a labaranhausa@corp.legit.com

Sanarwa na musamman: Shafin NAIJ Hausa ya koma Legit Hausa

Asali: Legit.ng

Tags:
Online view pixel