A karshe: 'Yan Kwankwasiyya sun yi magana a kan zarginsu da cin mutuncin Pantami

A karshe: 'Yan Kwankwasiyya sun yi magana a kan zarginsu da cin mutuncin Pantami

- A ranar Talata ne wasu matasa da ake kyautata zaton magoya bayan kungiyar Kwankwasiyya ne suka ci mutuncin ministan sadarwa, Dakta Isa Pantami, a Kano

- A cikin wani faifan bidiyo da ke yawo a kafafen sadarwa da dandalin sada zumunta, an ga wasu matasa na yi wa Pantami ihun ba ma yi tare da dora masa jar hula a ka

- Shugaban jam'iyyar PDP a Kano kuma jigo a tafiyar Kwankwasiyya ya ce yaransu ne suka ceci Pantami daga cin mutuncin da matasan ke shirin yi masa

Jigo a tafiyar kungiyar Kwankwasiyya kuma shugaban jam'iyyar PDP a jihar Kano, Injiniya Rabi'u Sulaiman Bichi, ya ce ba mambobinsu ne suka ci mutuncin ministan sadarwa na kasa, Dakta Isa Pantami, ba ranar Talata a Kano.

Bichi na wadanann kalamai ne bayan bullar wani faifan bidiyo a dandalin sada zumunta inda aka ga wasu matasa sanye da jajayen hula na yiwa Minista Pantami ihun bama yi tare da dora masa jar hula a ka.

Da yake mayar da martani a kan faruwar lamarin, Bichi ya bayyana cewa yaransu masu biyayya ne da son zama lafiya tare da dora alhakin faruwar lamarin a kan abokan hamayyarsu da ke son bata musu suna.

DUBA WANNAN: Masu garkuwa da mutane sun sace babban ma'aikacin CBN, Mustapha Sulaiman Hunkuyi

"Yaranmu masu son zaman lafiya ne, ba zasu yi wani abu da kan iya haifar da rikici ba. Aikin abokan hamayya da ke son bata mana suna ne.

"Mun je filin jrgin ne domin raka daliban mu da gidauniyar Kwankwasiyya ta dauki nauyinsu zuwa karatu a kasashen ketare, a saboda haka matasan da suka aikata cin mutuncin ba tare suke da mu ba," a cewar Bichi.

Shugaban jam'iyyar ya kara da cewa magoya bayan Kwankwasiyya ne suka ceci minista Pantami daga sharrin matasan da suka ci masa mtunci a filin tashi da saukar jirage na Mallam Aminu Kano da ke birnin Kano.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel