Karin wa'adin aiki ga sakatarorin gwamnati 7 da zasu yi murabus rashin adalci ne, in ji wasu daraktoci

Karin wa'adin aiki ga sakatarorin gwamnati 7 da zasu yi murabus rashin adalci ne, in ji wasu daraktoci

- Gunaguni da bacin rai sun biyo bayan karin wa'adin aiki da shugaban kasa Muhammadu Buhari ya yi wa wasu sakatarorin gwamnati 7

- Daraktocin da suka bukaci a sakaya sunansu, sun ce farantawa mutane kadan ne amma muzgunawa da yawa ne

- Hakan kamar yana nuna su kadai suke da nagarta da kwarewar aiki ne, in ji daraktocin

Daraktoci da mataimakansu a ma'aikatar tarayya sun nuna damuwarsu akan karin wa'adin aiki da shugaban kasa Muhammadu Buhari ya yi wa manyan sakatarorin gwamnati 7 a ranar Laraba.

Manyan ma'aikata a ofishin sakataren gwamnatin tarayya, ofishin shugaban ma'aikata, ma'aikatar harkokin waje da sakateriyar tarayya a jiya sun bayyana bacin ransu akan batun.

A watanni 18 da suka gabata, majalisar wakilai ta nuna damuwarta akan irin karin wa'adin aikin nan da aka yi wa Dr Jamila Shu'ara, babbar sakatariyar ma'aikatar man fetur ta lokacin.

Tuni suka umarci shugaban ma'aikatan ta lokacin, Winfred Oyo-Ita da ta karbi duk albashin da aka biya Shu'ara.

KU KARANTA: Innnalillahi wa inna ilaihirraji'un: Allah ya yi wa wani tsohon kwamishinan lafiya a jihar Kaduna rasuwa

Wasu daraktocin da ba zasu fadu ba saboda yanayin rahoton sun ce babu adalci a karin wa'adin.

Sun ce adalci shi ne a bar manyan sakatarorin masu murabus su tafi ba wai a nuna musu ba za a iya rabuwa dasu ba.

"Idan da sauran da suka yi murabus na nan har yanzu, babu yadda zasu iya kai matsayin manyan sakatarorin. Wannan kuma na nuna cewa kamar su kadai ne suka cancanta," daya daga cikin daraktocin da ya yi magana da Daily Trust a Abuja.

"Mu masu biyayya ne kuma wajibi ne mu bi duk abinda gwamnati mai mulki ta ce. Amma take dokar kasa don farantawa wasu kalilan tare da batawa mutane da yawa rai bashi da dadi," In ji wani daraktan.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel