Tarar biliyan $9: Lauyoyin Najeriya sun samu muhimmiyar nasara a kotun kasar Ingila

Tarar biliyan $9: Lauyoyin Najeriya sun samu muhimmiyar nasara a kotun kasar Ingila

A ranar Alhamis ne wata kotun harkokin kasuwanci da ke kasar Ingila ta sahale wa Najeriya ta daukaka kara a kan hukuncin biyan tarar biliyan $9.6 ga kamfanin P&ID (Process and Indutrial Development Limited).

Tawagar lauyoyin Najeriya ta nufi kotun ne domin neman ta dakatar da hukuncin da kotun da ke kasar Ingila ta yanke.

Ministan shari'a kuma jagoran tawagar lauyoyin Najeriya da suka tafi kasar Ingila ne ya tabbatar da hakan ga manema labarai.

A ranar Laraba, 25 ga watan Satumba, shugaba Buhari ya yi korafin cewa ana son a cuci Najeriya ta hanyar yanke hukuncin tilasta kasarsa biyan kamfanin P&ID makudan kudade.

Shugaba Buhari ya bayyana hakan ne a daya daga cikin jawaban da ya gabatar a wurin taron kasa da kasa a kan muhalli wanda ya gudana a kasar Amurka.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel