Rundunar sojin Najeriya tayi kaca-kaca da sasanin yan Boko Haram a Borno

Rundunar sojin Najeriya tayi kaca-kaca da sasanin yan Boko Haram a Borno

Rundunar sojin saman Najeriya ta lalata babban sansanin horo da wajen ajiye kayayyakin yan ta’addan Islamic State of West Africa Province (ISWAP) a Kusuma a gezar tafkin Chad da ke Borno.

Daraktan hulda da jama’a na rundunar sojin, Ibikunle Daramola, ya bayyana hakan a wani jawabi da ya saki a ranar Alhamis, 26 ga watan Satumba a Abuja.

Mista Daramola yace rundunar Operation lafiya dole ce ta gudanar da aikin a ranar Laraba, 25 ga watan Satumba.

“An kai farmakin ne bayan samun bayanai na kwararru wanda ya nuna cewa wani bangare na wajen ya kasance sansanin horo na yan ta’addan.

“Yayinda suke amfani da wasu gine-gine a sansanin wajen ajiye man fetur, makama da kuma alburusai da sauran kayayyakin da ake kawo masu.

“Kafin kai harin an gano wasu mayaka na kokarin tserewa daga waje a lokacin da suka jiyo karar jirgin sama.

“Sun yi rashin nasara inda wasu da dama daga cikinsu suka mutu a harin.

KU KARANTA KUMA: Innnalillahi wa inna ilaihirraji'un: Allah ya yi wa wani tsohon kwamishinan lafiya a jihar Kaduna rasuwa

“An kuma yi kaca-kaca da wajen ajiye kayayyakin nasu, inda wajen ya tashi da wuta sakamakon mamayyar,” inji shi.

Kakakin sojojin yace rundunar sojin saman za ta ci gaba da kokarinta na lallasa sauran yan ta’addan da suka rage a Arewa maso Gabas.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel