Masu garkuwa da mutane sun sace babban ma'aikacin CBN, Mustapha Sulaiman Hunkuyi

Masu garkuwa da mutane sun sace babban ma'aikacin CBN, Mustapha Sulaiman Hunkuyi

- Wasu 'yan bindiga sun yi awon gaba da Mustapha Sulaiman Hunkuyi, wani babban ma'aikaci a babban bankin kasa (CBN)

- Dauda Hunkuyi, dan uwa ga Mustapha ya tabbatar da faruwar lamarin tare da bayyana cewa masu garkuwa da mutanen sun nemi makudan kudin fansa

- Ana yawan samun matsalar sace mutane a kan manyan hanyoyin da ke sassan Najeriya, musamman babbar hanyar Abuja zuwa Kaduna

Wasu 'yan bindiga da ya zuwa yanzu ba a san ko su waye ba sun sace ma'aikacin babban bankin kasa (CBN), Mustapha Sulaiman Hunkuyi, a daren ranar Laraba.

Da yake tabbatar da sace ma'aikacin ga jaridar Daily Nigerian, Dauda Hunkuyi, dan uwa ga tsohon sanatan jihar Kaduna, Sulaiman Hunkuyi, ya ce 'yan bindigar sun kira su tare da neman makudan kudin fansa.

Sai dai, Dauda bai ambaci adadin kudin da masu garkuwa da Mustapha suka nema ba.

DUBA WANNAN: An kama kurtun soja da kananan buhunhunan tabar wiwi 169 a Jigawa

An samu mabanbantan bayanai dagane da wurin da aka sace Mustapha. A yayin da rahotanni suka bayyana cewa an sace shi ne a kan babbar hanyar Abuja zuwa Lokoja, majiyar cikin gida ta ce an sace shi ne a kan hanyar Katsina zuwa Kano.

Ana yawan samun matsalar sace mutane a kan manyan hanyoyin da ke sassan Najeriya, musamman babbar hanyar Abuja zuwa Kaduna.

An sace daruruwan 'yan Najeriya a 'yan watannin baya bayan nan, kuma an yi kiyasin cewa an biya makudan kudi kafin masu garkuwa da mutane su sake su.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel