Wani mutumi ya haikewa abokiyar aikinsa har lahira, ya kuma boye gawar ta

Wani mutumi ya haikewa abokiyar aikinsa har lahira, ya kuma boye gawar ta

Rundunar yan sanda reshen jihar Ogun ta kama wani dan shekara 27 mai su a Eniola Adenuga, bisa zargin yiwa abokiyar aikinsa mai suna Faith Jude fyade har lahira a yankin Lafenwa dake kudancin karamar hukumar Abeokuta.

Kwamishinan yan sandan jihar, Bashir Makama ya gurfanar da mai laifin tare da wasu mutane 18 wadanda aka kama bisa laifuffuka daban daban wadanda suka hada da fyade, fashi da makami da yan kungiyar asiri da sauran su, a hedikwatan rundunar da ke Eleweran, Abeokuta a ranar Laraba, 25 ga watan Satumba.

Kwamishinan wanda ya samu wakilancin mataimakin kwamishinan yan sanda na sashin ayyuka, Edward Ajogun yace an kama Adenuga, ma’aikacin na’urar samar da kudi da laifin kisa bayan ya e kai rahoton ganin gawar Faith a ofishin yan sanda a Lafenwa.

Yace mai laifin ya aikata laifin ne a ranar 16 ga watan Satumba, amman ya kai rahoton gawar abokiyar aikin tasa a ranar 19 Satumba.

Kwamishinan yan sandan yace mai laifin ya bayyana ma jami’an yan sanda a ofishin yan sanda cewa ya samu gawar abokiyar aikinsa rufe da wani lema a gaban shagon su.

A cewar Makama, mai laifin yayi amfani da daman ruwan sama da aka yi a ranar da lamarin ya ya auku, ya toshe ma marigayiyar baki da kyalle don hana ta yin kururuwa yayin da yake yi mata fyade.

Ya bayyana cewa Adenuga ya ajiye gawar marigayiyar a shagonsa har na tsawon kwana uku bayan aukuwar lamarin, amman daga karshe ya kai kara saboda tsananin warin dake fita daga gawar.

Makama ya kara da cewa mai laifin ya karbi baki akan aikata laifin bayan yan sanda sun azabtar da shi.

KU KARANTA KUMA: Masu garkuwa da mutane sun sace wata sabuwar amarya a hanyarta ta zuwa Sokoto

Adenuga yayi ikirarin cewa yana nadama akan abunda ya aikata, ya roki gwamnatin da tayi hukuncin da jin kai.

Kwamishinan yan sandan ya bayyana cewa reshen na cigaba da gudanar da farautar masu laifi da sansaninsu a jihar.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel