Innnalillahi wa inna ilaihirraji'un: Allah ya yi wa wani tsohon kwamishinan lafiya a jihar Kaduna rasuwa

Innnalillahi wa inna ilaihirraji'un: Allah ya yi wa wani tsohon kwamishinan lafiya a jihar Kaduna rasuwa

- Allah ya yi wa tsohon kwamishinan lafiya na jihar Kaduna rasuwa

- Tsohon likitan ya rasu ne sa'o'in farko na yau Alhamis a babban asibitin kasa dake Kaduna

- Za a yi jana'izarsa kamar yadda addinin islama ya tanadar a masallacin sultan Bello da ke Kaduna

Allah ya yi wa tsohon kwamishinan lafiya na jihar Kaduna, Dr. Abdullahi Muhammad Tukur rasuwa.

Ya rasu ne a babban asibitin kasa dake Abuja a sa'o'in farko na ranar Alhamis kamar yadda jaridar Daily trust ta ruwaito.

Za a yi jana'izarsa kamar yadda addinin musulunci ga tanadar a masallacin Sultan Bello da ke Kaduna.

KU KARANTA: Sabbin kirkire-kirkire ne hanyar inganta aikin gwamnati, in ji Yemi-Esan

Za a birnesa a makabartar musulmai da ke Unguwan Sarki.

Tsohon babban likita ne a ma'aikatar lafiya tsakanin 1972 zuwa 1975.

Bayan nan ne ya rike kujerar kwamishinan lafiyan jihar tsakanin 1976 zuwa 1978.

Marigarin ya shugabanci hukumar lafiya ta jihar Kaduna daga 1980 zuwa 1983. Bayan nan ne ya yi murabus inda ya bude asibitinsa a cikin garin Kaduna.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel