Magu: Wasu na tattara duwatsu a buhu a matsayin takin zamani

Magu: Wasu na tattara duwatsu a buhu a matsayin takin zamani

Mukaddashin shugaban hukumar EFCC mai yaki da masu yi wa tattalin arzikin kasa zagon-kasa, Ibrahim Magu, ya ce masu zuba kasa a cikin buhu su na saidawa a matsayin takin zamani.

Da Ibrahim Magu ya ke jawabi a wajen wani taro a Kaduna, ya bayyana cewa ana yin wannan danyen aiki ne a karkashin tsarin noman da babban bankin Najeriya na CBN ta shigo da shi kwanaki.

Mista Ibrahim Magu ya yi wannan jawabi ne a wajen wani taro da hukumar HEDA ta shirya domin yaki da rashin gaskiya a Najeriya. Wilson Uwujaren, shi ne ya wakilci Ibrahim Magu a taron.

Kakakin na EFCC da ya ke jawabi a madadin Mukaddashin shugaban hukumar ya ce sun samu rahoto daga bakin mutane game da irin barnar da ake shiryawa a wannan tsari aikin noma na CBN.

KU KARANTA: Najeriya ta buga sahun asara a dalilin shiga wata yarjejeniyar wuta

Hukumar ta EFCC ta ce duk matsalolin da ke faruwa a kasar ba su rasa nasaba da satar dukiyar jama’a da ake yi. Magu ya sha alwashin sun tattaro duk wani kudin sata sun maida ga masu su.

Wannan shi ne taro karo na 15 da hukumar Human and Environmental Development Agenda mai rajin kare Bil Adama wanda aka fi sani da HEDA ta shirya. An yi zaman ne a Ranar 24 ga Satumba.

“Ya kamata kungiyoyi masu zaman kansu su kara kokari a wannan lamari. Ba mu son ganin barnar ta yi kaimi. A tsarin noman da aka kawo, wasu na saida kasa da sunan taki” Inji Uwujaren.

Bayan zargin mutanen da ke dinke kasa su na saidawa a matsayin taki. A daidai wannan lokaci gwamnatin shugaba Muhammadu Buhari ta dage domin ganin mutanen kasar sun koma gona.

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewa tare da mu.

Ga masu bukatar manhajar mu na Musulunci sai a bibiyi wannan shafi

https://fb.gg/play/ramadan_ramadan

Asali: Legit.ng

Online view pixel