Rashin ingantaccen jagoranci ne dalilin da ya hana Najeriya cigaba – Shugaban NUC

Rashin ingantaccen jagoranci ne dalilin da ya hana Najeriya cigaba – Shugaban NUC

Shugaban Hukumar tantance Jami’o’in Najeriya wadda aka sani da NUC, Farfesa Abubakar Rasheed a jiya Laraba 25 ga watan Satumba ya bayyana ta’allaka rashin cigaban Najeriya bisa dalilin rashawa da kuma shugabanci maras nagarta.

Ya fadi wannan maganar ne a ma’aikatar harkokin kasashen wajen Najeriya dake Abuja a wurin wani taron na musamman domin murnar ranar ma’ikatan Najeriya na shekarar 2019.

KU KARANTA:Yanzu-yanzu: ‘Yan bindiga sun kashe wasu matafiya a kan hanyar Abuja

A cewarsa, rashin samun shugabanci mai nagarta ne dalilin da yasa tattalin arzikin Najeriya ya kasa daidaituwa wanda hakan ke sa ‘yan kasar na tsallakawa kasashen ketare.

Ya kara da cewa, kokarin da gwamnatin da ta shude ta yi ya kasa samar da abinda ake bukata a dalilin rashawa, wawurar dukiyar jama’a da kuma gazawar gwamnatin ita kanta.

A bangare guda kuwa, Mukkadashiyar Shugaban ma’aikatan Najeriya, Dr Folashade Yemi Esan ta yi kira ga ma’aikatan gwamnatin da su dage a kan ayyukansu domin bada gudunmuwarsu wurin cigaban kasa.

A wani labarin kuwa, mun ji cewa ‘yan bindiga sun kashe wasu matafiya a kan hanyar Lokoja-Abuja a yammacin ranar Talata 24 ga watan Satumba.

Wani wanda abin ya faru a kan idonsa ya bamu labarin cewa, ‘yan bindigan suna sanye ne da tufafin sojoji inda suka budewa mota kirar Sharon wuta har ta wuntsula a dalilin fasa tayarta da aka da bindiga.

Ku biyo mu a https://facebook.com/legitnghausa

ko a http://twitter.com/legitcomhausa

KU LATSA: Hanyar sauko da sabuwar manhajar jaridar Legit.com Hausa cikin sauki

Ga masu shawara ko korafi, a same mu a labaranhausa@corp.legit.com

Sanarwa na musamman: Shafin NAIJ Hausa ya koma Legit Hausa

Asali: Legit.ng

Online view pixel