Wasu gawarwaki sun ga ta kansu yayin da aka kwakwalo su daga kabari wata daya da binne su akan rabon gado

Wasu gawarwaki sun ga ta kansu yayin da aka kwakwalo su daga kabari wata daya da binne su akan rabon gado

- Wasu mutane da suka mutu sun ga ta kansu, yayin da magada suka je har kabarinsu suka kwakwalo su akan rabon gadon wani fili

- Wadannan mutane dai sun mutu shekaru shida da suka gabata, amma saboda rikicin rabon gadon filin da suka mutu suka bari ya saka ba a binne su ba

- Sai dai kuma makonni uku da suka gabata an binne mamatan, amma wasu daga cikin magadan suka ce Allan fur ba su yadda ba sai an kammala rikici za a binne su, hakan yasa suke je suka tono su daga kabari

Wani rikici da ya barke a tsakanin wasu mutane ya fito da wani sabon salo akan wani filin gado da wasu mutane suka mutu suka bari, wannan rikici ya jawo daya daga cikin mutanen da suke rigimar ya tono gawarwakin mutanen da suka mutu suka bar filayen mako uku bayan binne su.

Wannan lamari dai ya faru a Isiozi Umuaka dake jihar Imo. An bayyana cewa gawarwakin da aka tono din na wata mata ce da surukarta wadanda suka mutu shekaru shida da suka gabata, amma kuma an ki binne su tun wannan lokacin saboda rikicin filin gadon.

KU KARANTA: Tirkashi: Mutane sun fito kwansu da kwarkwatarsu suna zanga-zanga saboda gwamnati za ta sanya dokar hana zina

Sai dai kuma mako uku da ya gabata, an binne su a cikin filin da ake rikicin, amma daya daga cikin mutanen da ake rikicin da su sun bayyana cewa ina babu wannan maganar domin kuwa har yanzu maganar rikicin filin tana kotu.

Hakan yasa suka kwakwalo su daga cikin kaburburan na su suka kuma dauki gawarwakin su zuwa tsakiyar kasuwa.

Mutane dai sunyi ta kace-nace akan wannan lamarin, inda wasu ke ganin wannan abu da magadan suka yi ga gawarwakin bai kamata ba, domin koma yayane dai su sun riga sun mutu babu wani abu da za su iya yi idan an bar su ba a binne su ba.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel