'Yan sanda sun kashe wani gawurtaccen dan fashi da ake nema ruwa a jallo

'Yan sanda sun kashe wani gawurtaccen dan fashi da ake nema ruwa a jallo

Rundunar 'yan sanda reshen jihar Taraba ta ce ta kashe wani gawurtaccen dan fashi da makami da ta dade tana nema ruwa a jallo.

A sanarwar da mai magana da yawun rundunar na jihar Taraba, David Misal ya fitar, ya ce an yi nasarar kashe dan fashin ne bayan an sanar da 'yan sanda cewa wasu 'yan bindiga sun tare hanyar Jatau/Borno kuru-Ku a karamar hukumar Bali na jihar Taraba suna yi wa mutane fashi.

A cewar sanarwar, 'yan sandan tare da hadin gwiwa 'yan kungiyar sa kai sun garzaya inda lamarin ke faruwa kamar yadda Channels TV ta ruwaito.

DUBA WANNAN: Masu garkuwa da mutane sun sace mataimakin shugaban karamar hukuma a Katsina

Sanarwar ta cigaba da cewa da ganin 'yan sandan, 'yan kungiyar fashi da makamin suka fara musayar wuta da 'yan sandan wadda hakan ya yi sanadiyar rasuwar gawurtaccen dan fashin yayin da sauran suke tsere da raunuka na harsashin bindiga.

Sanarwar ta kuma ce 'yan sandan sun kwato bindiga kirar pistol da harsashi da layyu da babur a wurin da aka aikata fashin.

Sanarwar ta bukaci al'ummar jihar su rika gaggawar sanar da 'yan sanda idan sun ga matsala domin daukan mataki cikin gaggawa domin jihar Taraba ba wurin buyar bata gari bane.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel