Ainihin dalilin da yasa sojoji suka rufe ofisoshin Mercy Corps

Ainihin dalilin da yasa sojoji suka rufe ofisoshin Mercy Corps

Rundunar sojojin Najeriya ta fara cika alkawari kan gargadin da tayi na rufe ofishin duk wata kungiya mai zaman kanra da ke da alaka da Boko Haram inda ta rufe ofisoshin mercy Corps da ke Arewa maso Gabashin kasar.

A yayin rufe ofishin Action Against Hunger (AAH) a makon da ta gabata, rundunar sojin ta gargadi sauran kungiyoyin cewa ba za tayi wata-wata ba wurin rufe su muddin ta gano suna da hannu cikin lamarin.

The Punch ta ruwaito cewa wata majiya daga kungiyoyin jin kai na arewa maso gabas, a ranar Laraba ta ce sojojin sun rufe ofishin Mercy Corp ne bayan wani direba da ke dauke da kifi da kudi naira miliyan 20 a motarsa ya ce kayan na Mercy Corp ne.

DUBA WANNAN: 'Yan sanda sun gano gawarwaki cikin manyan kaburbura a Benue

Majiyar ta ce, "Direban ya yi tsamanin za a bar shi ya wuce ne bayan ya ambaci sunan Mercy Corp amma sojojin suka bincika motar inda suka gano makuden kudin a boye da kifin da ya ke dauke da shi."

Ya ce nan take sojojin suka rufe ofisoshin Mercy Corp da ke Gwoza, Damboa, Maiduguri da Damaturu.

A bangaren ta, Action Against Hunger ta ce 'ba ta amince da zargin da rundunar sojin ke yi mata ba na tallafawa 'yan ta'adda.'

A sanarwar da ta fitar a ranar Laraba, ta ce tana aiki da wasu mahukunta a Najeriya domin warware matsalar.

Anyi yunkurin ji ta bakin mai magana da yawun Operation Lafiya Dole, Kwanel Ado Isa domin jin dalilin rufe ofisoshin Mercy Corp a jihohin Borno da Yobe amma hakan ya ci tura domin bai amsa wayarsa ba kuma bai amsa sakon tes din da aka aike masa ba a lokacin hada wannan rahoton.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel