Bill Gates ya bayyana abinda yafi bashi mamaki game da Dangote

Bill Gates ya bayyana abinda yafi bashi mamaki game da Dangote

Fittacen attajirin kasar Amurka Bill Gates ya bayyana abinda ya fi bashi mamaki game da Alhaji Aliko Dangote, shugaban Dangote Group.

An yayin taron 'Gaolkeepers Summit' da aka gudanar a binrin New York a ranar Laraba, an tambayi Gates da Dangote su fadi abubuwan da ya fi ba su mamaki game da juna kamar yadda The Cable ta ruwaito.

Da ya ke amsa tambayar, Gates ya ce: "Munyi farin cikin haduwa da juna, idan muna tafiya cikin Legas mu kan samu lokacin yin hira sosai saboda cinkoson motoci a birnin. Na kan rika nuna wa Aliko wasu alkalluman bincike na da aka gudanar, misali na kan fada masa cewa ya kamata a inganta rigakafi a Sokoto ko ya dace Kano tayi kaza...".

DUBA WANNAN: Yanzu-yanzu: Osinbajo ya bukaci Google ta janye wani faifan bidiyonsa da aka wallafa a YouTube

"Aliko ya san mutane sosai kuma ya iya hulda da al'umma. Sai dai kaji yace bari mu kira gwaman' kafin ka ce wani abu sai kaji muna magana da gwamnan Sokoto a waya kan lamarin.

"Wannan baiwar da ya ke da ita na kula kyakyawar alaka da al'umma ya taimakawa Aliko ya bunkasa - ka san ni kuma mutum ne mai kunyar kiran mutane, nafi son in aika sakon email kawai.

"A dalilin hakan, ni da Aliko mu kanyi waya tare da gwamnonin jihohin arewa shida sau biyu a shekara domin tattaunawa kan nasarar da ake samu na yin rigakafi.

"Babban kalubale ne amma muna amfani da baiwar Aliko na iya magana da kyakyawar alakar da ya ke da shi da al'umma kuma baya tsoron kiran kowa. Kowa na son yin magana da shi, abin ban sha'awa ne."

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel