Muna amfani da inifam dinmu wajen fashi a manyan tituna – Korarrun sojoji

Muna amfani da inifam dinmu wajen fashi a manyan tituna – Korarrun sojoji

A ranar Talata, 24 ga watan Satumba, bayanai na gaskiya sun billo kan yadda wasu korarrun jami’an sojojin Najeriya ke gudanar da miyagun ayyukansu a manyan tituna.

Sunayen yan ta’addan sune Ndidi Oluchukwu, Owolabi Adeyemo, David Olufemi, Iseyin Samuel Isreal, Emeka Ibeh, Samuel Anochime da kuma Ebedot Stephen, jaridar Guardian ta ruwaito.

Daya daga cikin sojojin, Oluchukwu, da yake zayyanarsa yace: “An sallame ni a bayana saboda na dauki uzuri daga kwamandan sashinmu na komawa gda domin na yi wa kaina magani. Na shafe sama da mako guda da aka bani.

Muna amfani da inifam dinmu wajen fashi a manyan tituna – Korarrun sojoji
Muna amfani da inifam dinmu wajen fashi a manyan tituna – Korarrun sojoji
Asali: Twitter

“Na koma gida sanna na dan tsaya na wani lokaci kafin na hade da wasu korarrun sojoji a Lagas. Na fara sabon rayuwana ta hanya raka motocin haya. Ina samun N3,500 a kullun. Na hadu da sauran tawagar yayinda nake raka motoci. Sai muka hade muka kafa wata sabuwar kungiya."

KU KARANTA KUMA: Ta bar babban tarihi a duniya: Wata mata 'yar shekara 40 ta mutu bayan ta haifi yara 69

Jami’an yan sanda wadanda suka kama sojojin sun bayyana cewa tawagar sun farma mutane inda suka badda kammani a matsayin OP MESSA.

Sannan, yan ta’addan kan yiwa mutane fashin motocisu da kayayyaki bayan sun nuna masu bindga sannan su tafi da motocin satan.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel