Masu garkuwa da mutane sun sace mataimakin shugaban karamar hukuma a Katsina

Masu garkuwa da mutane sun sace mataimakin shugaban karamar hukuma a Katsina

Masu garkuwa da mutane sun yi awon gaba da mataimakin shugaban karamar hukumar Charanchi na jihar Katsina, Aminu Hassan kamar yadda Daily Trust ta ruwaito.

Wasu mutane da ba a san ko su wanene ba suka sace Hassan daga kauyensu, 'Yan Albasa a daren ranar Talata.

Wasu na kusa da iyalansa sun ce Hassan na tare da iyalansa lokacin da mutanen suka dira gidansa suka yi awon gaba da shi.

Kakakin 'yan sandan jihar, SP Isha Gambo ya tabbatar da afkuwar lamarin inda ya ce 'yan sanda sun bazama cikin daji da niyyar ceto shi.

DUBA WANNAN: 'Yan sanda sun gano gawarwaki cikin manyan kaburbura a Benue

Ya ce, "Muna bibiyar sahunsu amma ba zan iya bayar da cikaken bayyani ba saboda tsaro amma ina tabbatar maka za a ceto shi."

A wani rahoton kuma, 'yan sandan sunyi nasarar kama mutane shida da ake zargin 'yan fashi da makami ne da suka dade suna cin karensu ba babbaka garin.

Gambo ya ce asirinsu ya tonu ne yayin da suka kai wa wani Alhaji Halilu Isiyaku na karamar hukumar Charanci hari yayin da ya ziyarci dan uwansa da ke fama da rashin lafiya a unguwar Tudun Matawalle.

Ya ce wadanda ake zargin sun amsa cewa sun aikata laifin kuma ana cigaba da zurfafa bincike.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel