Abin da ya sa mu ka ce an yi kuskure a shari’ar zaben 2019 – Lauyoyin PDP

Abin da ya sa mu ka ce an yi kuskure a shari’ar zaben 2019 – Lauyoyin PDP

‘Dan takarar jam’iyyar PDP a zaben 2019, Atiku Abubakar, ya daukaka kara gaban kotun koli a cikin makon nan a game da shari’ar da kotun da ke sauraron korafin zaben na bana su ka bada.

Lauyoyin ‘Dan takarar, a karkashin Dr. Livy Uzoukwu, sun gabatar da sabon korafi inda su ka bada hujjoji 66 da ya kamata a duba wajen tsige shugaban kasa Muhammadu Buhari daga mulki.

Alhaji Abubakar ya fadawa kotun koli su duba irin tarin dalilan da su ka bada a kuliya domin a rushe zaben shugaban kasa na 2019, inda su ka yi ikirarin APC ta sha kasa da kuri’a miliyan 1.6.

Tun da farko Atiku yace shugaba Buhari ya yi wa hukuma karya wajen cike fam din CF001 da ya gabatar gaban INEC. Lauyoyin PDP sun ce a kan hakan kadai sai a tunbuke shugaba Buhari.

Lauyoyin na PDP sun ce Alkalan da su saurarin karar zaben sun yi babban kuskure na cewa babu shaidar da ke nuna Vuhari ya yi karya domin kuwa shugaban kasar bai nuna wata shaida ba.

KU KARANTA: Tinubu ya fadi abin da ya sa Buhari ya doke Atiku a kotun zabe

Atiku ya kuma yi gardama a game da yadda kotu ta amince da banbancin sunan da aka samu a takardun shugaban kasa inda ya ce babu inda ya taba amfani da Mohamed Buhari a rayurwarsa.

A cewar manyan Lauyoyin ‘dan takarar shugaban kasar, kotun daukaka kara tayi kure da ta ce za a iya gudanar da zabe ba tare da an yi amfani da na’urorin da ke tantance masu kada kuri’a ba.

Atiku ya kuma yi ikirarin cewa duk shaidun da Buhari ya gabatar, babu wanda ya iya bada tabbacin ya na da takardun karatu. Lauyoyin sun ce an yi kuskure wajen yin watsi da wannan.

Lauyoyin jam’iyyar PDP sun fadawa kotun koli cewa Alkalan karamin kotun sun yi kuskure da su kayi fatali da batun kuri’un da aka soke a zaben wanda su ka ce ya taimaka wajen ba APC nasara.

Wadanda Lauyoyin na PDP su ke tuhuma a karar bayan shugaban kasa Muhammadu Buhari su ne hukumar zabe mai zaman kan-ta watau INEC da kuma jam’iyyar APC mai mulki a Najeriya.

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewa tare da mu.

Ga masu bukatar manhajar mu na Musulunci sai a bibiyi wannan shafi

https://fb.gg/play/ramadan_ramadan

Asali: Legit.ng

Online view pixel