Innalillahi: Ana kashe Musulmi ana cire sassan jikinsu a sanyawa 'yan wasu addinin a kasar China

Innalillahi: Ana kashe Musulmi ana cire sassan jikinsu a sanyawa 'yan wasu addinin a kasar China

- Ana cire sassan jikin mutane a gidan yari a kasar China ana sanyawa wasu mutane

- An kashe mutane masu tarin yawa a kasar wadanda suka hada da Musulmi 'yan kabilar Uighur

- Ana cire sassan jikinsu irin su zuciya, ido, da hunhu a sanyawa marasa lafiya na wani addinin

- Masu bincike sun yi kira ga majalisar dinkin duniya da ta dauki matakin gaggawa akan wannan lamari

Ana zargin kasar China da kashe mutanen da addininsu ba shi da karfi su cire sassan jikinsu su sanyawa wasu mutanen na wani addinin.

An kashe dubunanan daruruwan mutane daga 'yan kabilar Falun Gong wadanda suke mafi akasarinsu Musulmai ne, an sanar da hakan ne ga kungiyar kare hakkin dan adam ta majalisar dinkin duniya a ranar Talatar nan da ta gabata.

An sanyawa wata kwamiti a kasar ta China da zata gabatar da bincike akan wannan lamari, inda aka bayyana cewa mutanen da suke wannan aika-aika sun shafe shekaru masu yawan gaske suna yi kuma har yanzu ba su daina ba.

KU KARANTA: Ta bar babban tarihi a duniya: Wata mata 'yar shekara 40 ta mutu bayan ta haifi yara 69

Mutanen suna cire sassan jikin mutanen irinsu zuciya, ido, hunhu da sauransu daga jikin mutanen da basu ji ba basu gani, inji mai magana da yawun majalisar dinkin duniyar Hamid Sabi.

Birnin Beijing ya karyata wannan zargi da kungiyar kare hakkin dan adam din take yi na cewa ana cire sassan jikin mutane wadanda akasari wadanda suke zaune a gidan yari.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel