Abin da ya sa mu ka ba Oshiomhole wa’adi na kukanmu – Shugabannin APC

Abin da ya sa mu ka ba Oshiomhole wa’adi na kukanmu – Shugabannin APC

Kungiyar shugabannin jam’iyyar na jihohin Najeriya sun bada wa’adin kwanaki goma ga shugaban jam’iyya na kasa, Kwamred Adams Oshiomhole, ya magance masu duk matsalolin su.

Kamar yadda Daily Trust ta kawo rahoto a yau Alhamis 26 ga Watan Satumban 2019, shugabannin jihohin jam’iyyar sun kawo wannan korafi ne ta bakin shugaban kungiyarsu, Ali Bukar Bolari.

Alhaji Ali Bukar Bolari ya ce wannan wa’adi da su ka sa ya fara aiki ne tun Ranar 23 ga Satumba. Bolari ya bukaci shugaba Adams Oshiomhole da majalisarsa ta NWC ta duba lamarinsu tun wuri.

Ali Bolari yake cewa an yi watsi da ‘ya ‘yan jam’iyyar tun bayan da aka lashe babban zaben 2019. Shugaban shugabannin jihohin jam’iyyar mai mulki ya ce su na da bukatar a sakawa kokarinsu.

Da yake hira da ‘yan jarida ta waya, Bolari ya nemi a rika ba su mukamai a dalilin kokarin da su ka yi a lokacin zaben da ya gabata tare da tunawa da Iyalin Jiga-jigan da su ka rasu ko aka sace.

KU KARANTA: Gwamnatin Buhari ta sake amincewa da wasu ayyuka a makon nan

Daga cikin kukan da wannan kungiya ta ke yi shi ne an watsawa asalin Iyayen gida jam’iyya wadanda su ka kafa ta kasa a ido, sannan kuma sun ce ba su ganin sakayyan kokarin da su ka yi.

Wannan kungiya ta manyan APC sun fitar da matsaya da sa hannun Ali Bolari da babban Sakatarensa Ben Nwoye, inda su ke kokawa da yadda aka yi watsi da tsarin da APC ta kafu a kai.

Har ila yau, shugabannin APC na fadin jihohin kasar sun yi Allah-wadai da yadda aka gaza nada sabon Sakataren jam’iyya na kasa tun bayan da Mai Mala Buni ya ajiye aiki ya zama gwamna.

Bolari da Nwoye a takardar da su ka fitar, sun yi korafi kan yadda ba a kula ‘ya ‘yan APC a wajen mukaman tarayya a dalilin rashin Sakataren jam’iyya wanda ya kamata ya yi aiki da SGF.

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewa tare da mu.

Ga masu bukatar manhajar mu na Musulunci sai a bibiyi wannan shafi

https://fb.gg/play/ramadan_ramadan

Asali: Legit.ng

Online view pixel