Masu garkuwa da mutane sun halaka babban jami’in Dansanda a hanyar Kogi-Abuja

Masu garkuwa da mutane sun halaka babban jami’in Dansanda a hanyar Kogi-Abuja

Wasu gungun yan bindiga da ake zargin masu garkuwa da mutane ne dake cin karensu babu babbaka a kan babbar hanyar Abuja zuwa Lokoja sun bude ma wata motar Sharon wuta inda suka kashe dukkanin fasinjojinta gaba daya.

Rahoton jaridar Daily Trust ta ruwaito wani shaidan gani da ido ya tabbatar da aukuwar harin inda yace lamarin ya faru ne a daidai garin Koton karfe ma jahar Kogi, kuma motar da yan bindigan suka bude ma wuta ta fito ne daga garin Fatakwal ta nufi Abuja.

KU KARANTA: El-Rufai zai samar da jiragen sama guda 2 domin jigilar fasinja zuwa Abuja

Shaidan ya kara a cewa da misalin karfe 5:58 na yammacin ranar Talata, 24 ga watan Satumba ne yan bindiga suka kai musu harin, yace shi ma da kyar ya tsallake rijiya da baya.

“A lokacin da direban motar Sharon da ya fito daga garin Fatakwal ya ankara da yan bindigan sun tare titi sanye da kayan Sojoji, sai ya yi kokarin tserewa, amma yan bindigan suka bude masa wuta, a dalilin haka tayar motarsa ta fashe, daga nan sai ta wuntsula har sai da ta kashe dukkanin fasinjojin dake ciki.

“Ganin haka ne yasa muka fahimci cewa yan bindiga ne ko kuma masu garkuwa da mutane, sai direban motarmu ya ja da baya, duk da haka suka cigaba da bude mana wuta, sun samu direbanmu a kafada, da wani fasinja da suke sameshi a kai.

“Da kyar muka isa ofishin Yansanda dake Gegu-Beki inda Yansandan suka taimaka mana suka wuce damu zuwa babban asibitin Kotonkarfe, daga nan kuma aka wuce damu zuwa cibiyar kiwon lafiya ta gwamnatin tarayya dake Lokoja.” Inji shi.

Da yake tabbatar da aukuwar lamarin, kwamishinan Yansandan jahar, Hakeem Busari ya bayyana cewa daga cikin fasinjojin motar da yan bindigan suka yi sanadiyyar mutuwarsu akwai wani babban jami’in dansanda mai mukamin ASP dan jahar Edo.

Ku biyo mu a https://facebook.com/legitnghausa

ko a http://twitter.com/legitnghausa

KU LATSA: Hanyar sauko da sabuwar manhajar jaridar Legit.com Hausa cikin sauki

Ga masu shawara ko korafi, a same mu a labaranhausa@corp.legit.com

Sanarwa na musamman: Shafin NAIJ Hausa ya koma Legit Hausa

Asali: Legit.ng

Online view pixel