Gwamnatin Tarayya ta gamu da asara a kwangilar igiyar wuta

Gwamnatin Tarayya ta gamu da asara a kwangilar igiyar wuta

Wani dogon bincike da jaridar Daily Trust ta yi ya nuna yadda gwamnatin tarayyar Najeriya ta yi asarar kudi har Dalar Amura miliyan 52, a kudin gida wannan adadi ya haura Naira Biliyan 18.

Najeriya ta tafka asarar ne a sanadiyyar gaza kula da layukan wuta masu kauri na “Fiber Optics.” A wani rahoto da ya shiga hannun Jaridar, kasar ta gamu da asara ne saboda yawan tabarbarewar wuta.

Najeriya ce ke da mallakar igiyoyin jan wutan lantarki da kamfanonin GenCos masu samar da wuta a kasar. Ita kuma Najeriya ce ke da alhakin jan wutar zuwa kamfanonin da ke rabawa watau DisCos.

Igiyoyin wutan Najeriya na “Fiber Optics” masu karfin kilovolt 220 sun haura tsawon kilomita 8300, yayin da sauran igiyoyi masu karamin karfi na kilovolt 132 su ke da tsawon kusan kilomita 9000.

An tsara wadannan igiyoyi ne domin rika kula da wutar lantarki. Sai dai bincike ya nuna cewa aikin da igiyoyin su ke yi bai wuce kashi 40% na ainihin abin da aka shirya ba, wanda hakan ya jawo asara.

KU KARANTA: Osinbajo ya rubutawa Google takarda ta janye wani bidiyonsa

Sau uku ana ba wani Kamfani na Siemens na kasar waje wannan aiki amma abin ya gagara. Tun a zamanin kamfanin NEPA ta na aiki a Najeriya aka fara bada wanan kwangila a cikin shekarar 2006.

Bayan an samu sauyi a kasar, aikin ya koma kan kamfanin TCN wanda ta sake bada kwangila domin a inganta karfin wadannan igiyoyi masu jan wuta. A wannan yarjejeniya aka rasa Naira Biliyan 14.

Haka zalika wannan yajejeniya da aka yi a karshe bai yiwu ba bayan an yi barnar kudi. Wannan ya sa a Agustan 2017 aka sake soke kwangilar. TCN ta nuna cewa hakan ya fi zama alheri ga Najeriya.

Yanzu dai gwamnatin shugaban kasa Muhammadu Buhari ta na da niyyar ganin an samu akalla megawatt 20, 000 na wutar lantarki a Najeriya. Ana so a cin ma wannan buri ne nan da shekarar 2025.

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewa tare da mu.

Ga masu bukatar manhajar mu na Musulunci sai a bibiyi wannan shafi

https://fb.gg/play/ramadan_ramadan

Asali: Legit.ng

Online view pixel