Yaki da ta’addanci: Sojojin Najeriya sun fada tarkon yan ta’adda, da dama sun halaka

Yaki da ta’addanci: Sojojin Najeriya sun fada tarkon yan ta’adda, da dama sun halaka

Sojoji da dama sun rigamu gidan gaskiya, tare da wasu da dama da suka bace aka nemesu aka rasa biyo bayan wani mummunan harin kwantan bauna da mayakan kungiyar ta’addanci na Boko Haram suka kai musu a jahar Borno.

Jaridar Daily Trust ta ruwaito yan ta’addan sun kai ma Sojojin Najeriya yayin da suke tafiya da ayarin motocinsu a kan babbar hanyar data hada Gubio da Magumeri cikin karamar hukumar Gubio ta jahar Borno, lamarin ya auku ne da misalin karfe 4:15 na yammacin Laraba, 25 ga watan Satumba.

KU KARANTA: El-Rufai zai samar da jiragen sama guda 2 domin jigilar fasinja zuwa Abuja

Majiyar Legit.ng ta ruwaito wata majiya daga matasa yan sa kai ya tabbatar da aukuwar lamarin, inda yace harin ya yi muni matuka, wanda hakan ya yi sanadiyyar mutuwar Sojoji da dama, wasu kuma sun samu rauni.

“Maharan sun yi amfani da manyan makamai da bindigu a kan kwamban motocin Sojojin, fiye da Sojoji 12 sun mutu a sakamakon harin, yayin da dama kuma suka samu nau’o’in raunuka daban daban.” Inji shi.

Haka zalika majiyar ya kara da cewa yan bindigan sun kwace tarin makamai da alburusai da dama daga hannun Sojojin, sa’annan sun yi awon gaba da wata babbar motar aiki mallakin Sojojin.

Sai dai duk kokarin da jaridar ta yi na samun tabbacin aukuwar lamarin daga bakin hukumomin Soja ya ci tura sakamakon sun ki amsa tambayar, amma dai a yan kwanakin nan yan ta’adda sun tsaurara kai hare hare a yankin Arewacin Borno, musamman ma a shiryyar Gubio.

Ku biyo mu a https://facebook.com/legitnghausa

ko a http://twitter.com/legitnghausa

KU LATSA: Hanyar sauko da sabuwar manhajar jaridar Legit.com Hausa cikin sauki

Ga masu shawara ko korafi, a same mu a labaranhausa@corp.legit.com

Sanarwa na musamman: Shafin NAIJ Hausa ya koma Legit Hausa

Asali: Legit.ng

Online view pixel