FEC ta yi na’am da kashe Naira Biliyan 310 a kan hanyar Kano-Katsina da wasu manyan tituna

FEC ta yi na’am da kashe Naira Biliyan 310 a kan hanyar Kano-Katsina da wasu manyan tituna

A daidai lokacin da shugaban kasa Muhammadu Buhari ya ke halartar taron majalisar dinkin Duniya, mataimakinsa, Farfesa Yemi Osinbajo ne ya jagoranci taron FEC na Ministocin kasar.

A zaman FEC da aka yi jiya Laraba, 26 ga Satumba, 2019, Yemi Osinbajo, a madadin gwamnatin Najeriya ya amince da wasu kwangilolin tituna a fadin kasar da za su ci kudi Naira biliyan 310.

Ministan ayyuka da gidaje, Babatunde Fashola, ya bayyanawa ‘yan jarida wannan bayan an kammala taron a fadar shugaban kasa. An raba ayyukan ne a cikin yankunan da ke fadin kasar.

A cewar Ministan majalisar zartarwar ta amince da Naira biliyan 79 na kudin da aka warewa titin Ibada zuwa Ilesa har Ife. Haka zalika titin Asaba zuwa Garin Onitsha zai ci akalla Biliyan 200.

KU KARANTA: ‘Yan Majalisar Najeriya sun gano badakalar kudi a Neja-Delta

A cikin ayyukan da aka amince da su a makon nan akwai titin Kano zuwa Katsina wanda aka warewa Naira 29.65. Kamfanin Messrs Julius Berger da Messrs Renold aka ba wadannan aiki.

Za a dauko aikin Kano zuwa Katsina ne tun daga Gidan Mutum Daya har zuwa yankin kamfanin karafunan Katsina Steel Rolling Mill. Tsawon hanyar ta kai kilomita 78 inji Ministan ayyukan.

A shekarar 2013 ne gwamnatin tarayya ta fara bada kwangilar titin Katsina zuwa Kano. A lokacin hanyar mai tsawon kilomita 152 layi guda ce kurum. Wannan ya sa aka nemi a kara fadada titin.

Karamin Ministan ilmi, Chukwuemeka Nwajiuba, a na sa bangaren ya bayyana cewa Ma’aikatarsa ta amince da Biliyan 1.833 domin TETFund ta gina wani sashen karatu a jami’ar tarayya ta Abuja.

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewa tare da mu.

Ga masu bukatar manhajar mu na Musulunci sai a bibiyi wannan shafi

https://fb.gg/play/ramadan_ramadan

Asali: Legit.ng

Online view pixel