Majalisa: Akwai cuwa-cuwar Naira Biliyan 76 a kwangilolin Neja-Delta

Majalisa: Akwai cuwa-cuwar Naira Biliyan 76 a kwangilolin Neja-Delta

Kwamitin majalisar wakilan tarayya da ya yi bincike a kan kwangilolin da hukumar NDDC ta yi watsi da su a yankin Neja-Delta ta nemi hukumar ta karbo wasu makudan kudi da aka karkatar.

Majalisar wakilan kasar ta ba hukumar NDCC umarni ta nemo Naira biliyan 68 da aka ware na kwangiloli da wasu ayyuka a yankin mai arzikin man fetur na kasar amma aka kare ba ayi ba.

Jaridar Daily Trust ta ce shugaban wannan kwamiti da ya yi aiki na musamman, Ossai ‎Nicholas Ossai, shi ya sa hannu a wannan takardar bada umarni a lokacin da kwamitin ya koma bakin aiki.

Honarabul Ossai ‎Nicholas Ossai mai wakiltar yankin jihar Delta a karkashin jam’iyyar PDP da wasu ‘yan majalisa irin su Hon. Suleman Abubakar Mahmud Gumi ne su ka yi wannan bincike.

A cewar Ossai ‎Nicholas Ossai, NDDC ta bada kwangiloli fiye da 600 a Neja-Delta wadanda ba tare da an bi ka’ida ba. Daga arshe dole hukumar ta soke wasu daga cikin wadannan tarin kwangiloli.

KU KARANTA: 'Yan Majalisar Sokoto na APC sun samu galaba a kan PDP

Wani jami’in hukumar ta NDDC ya fadawa ‘yan majalisar tarayyar wannan da bakinsa a lokacin da su ka kira wani zama. Jami’in na NDDC yace kwangiloli 342 da aka bada ba su je ko ina ba.

Wannan ya sa wannan kwamiti ta nemi duk tsofaffin Darektocin NDDC su bayyana a gaban majalisa a zaman da za a yi yau 26 ga Watan Satumban 2019 domin cigaba da binciken badakalar.

Daga shekarar 2008 zuwa 2018, NDDC ta bada kwangilolin da su ka ci N2, 832, 611, 325, 966 inda ta kuma samun takardun shaida N1, 848, 774, 602,103 a cikin wadannan shekaru goma da aka yi.

Honarabul Suleman Abubakar Mahmud Gumi wanda ya na cikin wannan kwamiti na musamman yace za su gabatar da rahoton irin barnar da NDDC ta tafka domin hukuma ta kama masu laifi.

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewa tare da mu.

Ga masu bukatar manhajar mu na Musulunci sai a bibiyi wannan shafi

https://fb.gg/play/ramadan_ramadan

Asali: Legit.ng

Online view pixel