An kashe wasu yara da laifin yin bayaha a titi a kasar Indiya

An kashe wasu yara da laifin yin bayaha a titi a kasar Indiya

An cafke wasu mutane biyu, Rameshwar Yadav da Hakim Yadav wadanda ake zargi da lakadawa wasu yara biyu dukan tsiya da har yayi sanadiyar salwantar rayukansu a garin Madhya Pradesh da ke yankin Tsakiyar kasar Indiya.

Jaridar BBC ta rawaito cewa, mutanen biyu da suka shiga hannu sun lakada wa yaran dukan tsiya ne saboda sun yi bahaya a kan titi kamar yadda 'yan sandan kasar suka bayyana.

Jami'an tsaron sun ce an kai wa Roshni mai shekaru 12 da Avinash mai shekaru 10 hari ne a ranar Larabar da ta gabata yayin da suke bahaya kusa da titin wani kauye da talauci na rashin bandaki a gida ya yi masu katutu.

Miliyoyin al'ummar kasar Indiya wanda ke fama da talauci na biyan bukatunsu ne a filin a sanadiyar rashin bandaki, lamari da ke barazanar jefa mata da kuma yara cikin hadari mai girman gaske.

KARANTA KUMA: Babu wata rabuwar kai a tsakanin Buhari da Osinbajo - Gwamnonin APC

Wani babban jami'in dan sanda na kasar, SP Rajesh Chandel, a yayin zanatawa da manema labarai ya ce wadanda ake zargi sun yi amfani ne da itace wajen lakadawa yaran biyu duk da har sai da suka ce ga garin ku nan.

A wani rahoto da jaridar Legit.ng ta ruwaito, wani matashi mai shekaru 35 a duniya, Badamasi Musa, ya kashe ta hanyar rataya a kauyen Kabomo da ke karkashin karamar hukumar Bakori ta jihar Katsina.

Sanarwa: Mun gode da kasancewarku tare damu yayin da shafin Naij.com Hausa ya sauya suna zuwa Legit.ng Hausa

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayarku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Domin shawara ko bukatar ba mu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.com

Ku biyo mu a shafukan mu na dandalin sada zumunta:

https://facebook.com/legitnghausa

https://twitter.com/legitnghausa

Asali: Legit.ng

Online view pixel