Babu wata rabuwar kai a tsakanin Buhari da Osinbajo - Gwamnonin APC

Babu wata rabuwar kai a tsakanin Buhari da Osinbajo - Gwamnonin APC

- Gwamnonin APC sun karyata rade-radin da ke yaduwa kan cewa ana rashin ga maciji tsakanin shugaban kasa Muhammadu Buhari da mataimakin sa, Yemi Osinbajo

- Gwamna Babajide Sanwo Olu na jihar Legas ya ce rahotanni na jita-jita da kuma marasa tabbas basu da wani tasiri a ma'aunin gwamnonin APC

A yayin watsi da jita-jita da rahotanni na rade-radi, gwamnonin jam'iyyar APC sun ce karya ne babu wata rashin jituwa da ke tsakanin shugaban kasa Muhammadu Buhari da kuma mataimakinsa, Farfesa Yemi Osinbajo.

Sabanin yadda ake ikirari a wasu lunguna da kafofin sadarwa na kasar nan, gwamnonin APC sun ce maganar rashin 'yar ga maciji tsakanin Buhari da mataimakin sa ba gaskiya bace, lamarin da ya ce in hakan ta kasance babu fadar shugaban kasa kenan a kasar.

Gwamnan jihar Legas, Babajide Sanwo-Olu, a yayin da tabbatar da kyakkyawar alaka da ke jagororin kasar, ya ce Osinbajo shi ne ya jagorancin zaman majalisar zartarwa da aka gudanar cikin fadar Villa a ranar Laraba, 25 ga watan Satumba.

KARANTA KUMA: Wani mutum ya kashe kansa a jihar Katsina

Sanwo Olu wanda ya bayyana hakan yayin kaddamar da kwamitin sadarwa na gwamnonin jam'iyyar APC, ya ce suna amfani ne da zance na tabbas ba na shaci fadi ba ko kuma jita-jita marasa tushe.

Sanarwa: Mun gode da kasancewarku tare damu yayin da shafin Naij.com Hausa ya sauya suna zuwa Legit.ng Hausa

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayarku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Domin shawara ko bukatar ba mu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.com

Ku biyo mu a shafukan mu na dandalin sada zumunta:

https://facebook.com/legitnghausa

https://twitter.com/legitnghausa

Asali: Legit.ng

Online view pixel