Najeriya ta tafka asarar $157.5bn a tsakanin 2003 zuwa 2012 - Buhari

Najeriya ta tafka asarar $157.5bn a tsakanin 2003 zuwa 2012 - Buhari

Kamar yadda jaridar The Punch ta ruwaito, shugaban kasa Muhammadu Buhari ya ce Najeriya ta tafka gagarumar asarar dukiya ta kimanin dala biliyan 157.5, wadda a cewarsa ta zurare ne a sanadiyar almundanar da ta auku a tsakanin shekarar 2003 zuwa 2012.

Shugaban na Najeriya ya ce wanna mummunar ta'asa da aka tafka a kasar ta yi sanadiyar jefa kasar cikin matsi na tatalin arziki da kuma jefa miliyoyin al'ummar kasar cikin kangi na talauci.

Furucin wannan sanarwa ta fito daga bakin mai magana da yawun shugaban kasa, Mista Femi Adesina, wanda ya ambato sanarwar da Buhari yayi a wani taro da hukumar yaki da rashawa ta dauki nauyi kan hadin gwiwar kasashen Afirka dake maida hankali kan kokarin dakile almundahana a kasashen yankin.

Buhari ya bayyana kauracewa biyan haraji a matsayin daya daga cikin matsalolin almundahanar kudade da kasashen Afirka ke fuskanta, inda ya hikaito alkalumman hukumar sa ido kan biyan haraji da kuma asusun bayar da lamuni na duniya IMF, da cewar kasashe masu tasowa na tafka asarar fiye da dala biliyan 200 a duk shekara, lamarin da ya alakanta da yadda manyan kamfanoni ke kauracewa biyan haraji ga gwamnatocin kasar da suke cin albarkacinta.

KARANTA KUMA: Girgizar kasa ta hallaka mutane 19 a Pakistan

A yayin da shugaban kasa Buhari ya yabawa wadanda suka dauki nauyin taron wanda jaridar Legit.ng ta fahimci cewa ya gudana ne a gefa guda na daban yayin da ake gudanar da taron majalisar dinkin duniya karo na 74, cikin birnin New York na kasar Amurka.

Mista Adesina ya ce shugaban kasar Zambia, Edgar Lungu, da kuma takwaransa na Habasha, Sahle-Work Zewde, sun halarci taron.

Sanarwa: Mun gode da kasancewarku tare damu yayin da shafin Naij.com Hausa ya sauya suna zuwa Legit.ng Hausa

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayarku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Domin shawara ko bukatar ba mu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.com

Ku biyo mu a shafukan mu na dandalin sada zumunta:

https://facebook.com/legitnghausa

https://twitter.com/legitnghausa

Asali: Legit.ng

Online view pixel