Har yanzu Kemi Adeosun ce ministar kudi a shafin yanar gizo na gwamnatin Najeriya

Har yanzu Kemi Adeosun ce ministar kudi a shafin yanar gizo na gwamnatin Najeriya

Bayan shekara guda da yin murabus, har yanzu tsohuwar ministan kudi ta Najeriya, Kemi Adeosun, tana cikin jerin 'yan majalisar zartarwa a shafin yanar gizon gwamnatin tarayya na www.nigeria.gov.ng.

Ana iya tuna cewa, a ranar 18 ga watan Satumban 2018 ne shugaban kasa Muhammadu Buhari ya maye gurbin Adeosun da Zainab Shamsuna Ahmed, a matsayin ministar kudin kasar, biyo bayan fuskantar matsin lamba ta mallakar shaidar yiwa kasa hidima ta bogi.

Hakazalika binciken jaridar The Punch ya tabbatar da cewa, jerin 'yan majalisar zartarwa na gwamnatin Najeriya a shafinta na yanar gizo ya kunshi sunan gwamnan jihar Ekiti, Kayode Fayemi, a matsayin ministan ma'adanai, watanni 16 bayan ya yi murabus.

Fayemi ya karbi ragamar ma'aikatar ma'adanai a ranar 11 ga watan Nuwamban 2011, inda kuma ya yi murabus a shekarar 2018 domin neman takarar gwamnan jihar Ekiti.

Wannan kuskure na rashin aiwatar da sauye-sauye a shafin na gwamnatin Najeriya bai takaita kadai ba a nan domin kuwa akwai Hajiya Amina Mohammed, wadda ta ajiye aiki bayan da aka nada ta mataimakiyar babban sakataren Majalisar Dinkin Duniya a ranar 28 ga watan Fabrairun 2017.

KARANTA KUMA: Emmanuella da sauran kananan yara 5 mafi shahara da suka fi sa'annin su kudi a Najeriya

Hajiya Amina ta rike mukamin ministar ma'aikatar kula da yanayi da muhalli daga ranar 11 ga watan Nuwambar 2015 har zuwa 15 ga watan Disamba na shekarar 2016.

Bincike na nuni da cewa, babu wani sabon sauyi dangane da sunaye da ma'aikatu da ministocin Buhari suka rika tun a wa'adin gwamnatinsa na farko, inda kawo wa yanzu wata guda kenan da kafa sabuwar majalisar zartarwa a kasar.

A ranar 21 ga watan Agsutan da ya gabta ne shugaba kasa Buhari ya rantsar tare da bai wa sabbin minstocinsa 43 makamar aiki, sai dai har yanzu gwamnatin ba ta sabunta rahotanni ba shafin na yanar gizo.

KARANTA KUMA: Ina fatan na rinka sadaukar da dukiya ta tamkar Bill Gates - Dangote

Har wa yau a shafin, akwai tsaffin ministoci da basu samu dawo wa ba cikin majalisar zartarwa ta gwamnatin Najeriya kuma har yanzu sunayensu na nan a matsayin ministoci a idon sauran al'ummomi na duniya.

Ire-iren tsaffin ministocin sun hadar da na kasafi da tsare-tsaren kasa, Udo Udoma, Mansur Dan Ali na tsaro, na sadarwa Adebayo Shittu, Audu Ogbeh na noma, na harkokin cikin gida Abdulrahman Danbazau, Ibe Kachikwu na man fetur da kuma Heineken Lokpobiri tsohon karamin ministan noma da raya karkara da sauransu.

Sanarwa: Mun gode da kasancewarku tare damu yayin da shafin Naij.com Hausa ya sauya suna zuwa Legit.ng Hausa

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayarku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Domin shawara ko bukatar ba mu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.com

Ku biyo mu a shafukan mu na dandalin sada zumunta:

https://facebook.com/legitnghausa

https://twitter.com/legitnghausa

Asali: Legit.ng

Online view pixel