Kudin kamfe na N90bn: Jaridar Vanguard ta nemi gafarar Osinbajo

Kudin kamfe na N90bn: Jaridar Vanguard ta nemi gafarar Osinbajo

Daya daga cikin manyan jaridu a Najeriya, Vanguard, ta nemi gafarar mataimakin shugaban kasa Farfesa Osinbajo biyo bayan kuskuren da ta tafka na wallafa wani rahoto marar tabbas da ke yin kazafi a gare shi gami da bata masa suna.

Jaridar Vanguard ta nemi gafarar Osinbajo bayan da ta wallafa wani rahoto da ya ke nuni da cewa, mataimakin shugaban kasar ya karbi kimanin naira biliyan 90 a hannun hukumar tattara haraji ta kasa wato FIRS domin yin kamfe a zaben 2023.

Vanguard a ranar 25 ga wannan wata na Satumba da muke ciki, ta wallafa wani rahoto da kanun labarai kamar haka; “N90Bn FIRS Election Fund: Osinbajo’s problem, not 2023 politics”, takaitacciyar ma'ana dai, kudin da Osinbajo ya karba na N90bn a hannun hukumar FIRS domin yakin zabe a 2023.

KARANTA KUMA: Ina fatan na rinka sadaukar da dukiya ta tamkar Bill Gates - Dangote

A yayin da ta bayyana nadamarta karara wajen neman yafiyar mataimakin shugaban kasa, jaridar Vanguard ta gano cewa rahoton da ta wallafa ba ya da wata madogara ta dalilai na tabbas, lamarin da ya sanya ta gaggauta cire rahoton daga shafinta na yanar gizo.

A sanarwar da jaridar ta fitar, ta ce tana neman gafarar mataimakin shugaban kasa Osinbajo, jam'iyyarsa ta APC da kuma hukumar tattara harajin kasar dangane da duk wani mawuyacin hali da ta jefa su ciki.

Sanarwa: Mun gode da kasancewarku tare damu yayin da shafin Naij.com Hausa ya sauya suna zuwa Legit.ng Hausa

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayarku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Domin shawara ko bukatar ba mu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.com

Ku biyo mu a shafukan mu na dandalin sada zumunta:

https://facebook.com/legitnghausa

https://twitter.com/legitnghausa

Asali: Legit.ng

Online view pixel