'Yan sanda sun gano gawarwaki cikin manyan kaburbura a Benue

'Yan sanda sun gano gawarwaki cikin manyan kaburbura a Benue

An gano manyan kaburbura da gawarwaki masu yawa cikinsu a kauyen Gbatse da ke karamar hukumar Usongo na jihar Benue.

The Punch ta ruwaito cewa kakakin rundunar 'yan sandan jihar DSP Cathrine Anene ta ce ba za ta iya tabbatar da rahoton ba a halin yanzu.

Da aka nemi tayi karin bayani, sai ta ce, "mene zai hana ba za ku jira zuwa gobe ba?"

DUBA WANNAN: 'Yan ta'adda sun mamaye kananan hukumomi 8 a arewacin Borno - 'Dan majalisa

Rahoton da aka samu daga garin ya ce kawo yanzu an hako gawarwaki guda uku.

An kuma ce 'yan uwan mamatan sun gano gawarwakin 'yan uwansun da aka kashe.

Rahoton ya kara da cewa akwai wasu kaburbura biyar da ba a tona ba.

Ku cigaba da bibiyar mu domin karin bayani ...

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel